Daga Hussaini Baba, Gusau
Kwamishanar Hukumar Zabe Mai Zaman kanta ta Kasa a Jihar Zamfara, Hajiya Asma’u Sani Mai Kudi Malumfashi ta ziyarci ’yan jarida a cibiyar su da ke Gusau wato (NUJ), a jiya Laraba.
Kwamishinar ta bayyana cewa “Gagarumar gudummuwa da ’yan jarida ke bayarwa na ci gaban al’umma, kuma da gudunmuwarku ne aka samu gagarumar nasara a zaben da ya gabata. Musamman ma a nan Jihar Zamfara, muna godiya. Kuma ina mai tabbatar muku da cewa wannan hukumar za ta yi aiki da ku kafada da kafada wurin ganin an samu nasara a zabe mai zuwa.” In ji ta
Kwamishinar ta yi kira ga al’ummar Jihar Zamfara da su ziyarci santocinsun domin amsar katin zabe, haka ma wadanda a wannan karon suke cika shekaru 18 kamar yadda doka ta tanada, da masu canjin gari ko suna da wadanda tasu ta bace, suna iya zuwa wadannan santocin domin su amsa.
Kwamishinar ta bayyana cewa babu rowan hukumarsu da nuna bambanci tsakanin jam’iyyun da ake dasu. “za mu yi aiki da kowacce jam’iyya, fatanmu shi ne samun gagarumar goyon baya da amsar katin zabe don samun nasara a zabe mai zuwa.”
Shi ma a nashi jawabin, babban Sakataren Hukumar Zaben, Abdullahi Adamu Guzangu ya bayyana cewa; “Yanzu haka hukumar ta hada kwamitin hadin gwiwa tsakaninta da gwamnati domin wayar da kan al’umma, wajen kara kaimi ga amsar Katin zabe. Kuma Hukumar Zaben ita ce ke daukar nauyin duk ayyukan da ke gudana a Santocin amsar Katin zabe da ke fadin jijhar.”
A daya bangaren kuwa, yayin da yake jawabi, shugaban kungiyar ‘yan jarida ta kasa, reshen jihar Zamfara, Kwamared Mainasara Ruwan Dorawa ya yaba wa kwamishinar akan ziyarar da ta kawo. Sannan ya ba ta tabbacin cewa ‘yan jarida a fadin jihar zasu yi aiki kafada da kafada da hukumar domin ganin an samu nasara a zabe mai zuwa.