Kwamitin Binciken Kashe-kashen Mashegu Zai Fara Aiki Gadan-gadan  

Neja

Daga Muhammad Awwal Umar,

Gwamnatin Jihar Neja ta kafa kwamitin binciken kashe-kashe a karamar hukumar Mashegu. Kwamitin da gwamnatin jihar ta kafa a ranar 3 ga watan Nuwambar shekarar 2021, domin yin bincike kan harin da ya janyo rasa rayuka da raunuka da yin garkuwa da mutane a kauyen Mazakuka da Kulhu da Adogon-Malam da ke karamar hukumar Mashegu, an nemi kwamitin ya saurari korafe-korafen jama’a kan faruwar lamarin.

 

A wata takardar da sakataren kwamitin, Malam Shafi’i Zakari ya sanyawa hannu, ya bayyana cewa daga nauyin da aka daura wa kwamitinsu shi ne na lalubo dalilin faruwar tashe-tashen hankulan wajen gano masu hannu a cikin kulla rikicin ko kungiyar da ta dauki nauyin kai harin da kuma sanin adadin wadanda suka rasa rayukansu ko suka ji rauni a lokacin harin.

A cewarsa, daga cikin aikin kwamitin har da bai wa gwamnati shawarwari a kan matakan da ya kamata ta dauka domin kaucewa kara faruwar lamarin a nan gaba.

 

Sakataren kwamitin wanda shi ne babban daraktan ayyuka na musamman, yayi kira ga al’umma da su gabatar da korafe-korafensu daidai da yadda tsarin aikin kwamitin zai gudana.

 

Ya bayyana cewa dukkan korafe-korafen a na iya gabatar da su a faifan CD ko makwafin flash dribe ko kuma a aika a yanar gizo ta adireshinsa kamar haka social commissions gmail.com zuwa ga sakatariyar kwamitin da ke lamba ta 14, Okada Road, Minna ta Jihar Neja ko kuma ofishin yanki na ma’aikatar shari’a da ke karamar hukumar Kontagora da Mashegu cikin kwanaki bakwai.

 

A cewar sakataren, kwamitin zai fara sauraren jin ra’ayoyin jama’a daga ranar 18 ga watan Nuwamba a gini mai lamba 14 kan hanyar Okada cikin garin Minna da misalin 11 na safe.

 

A lokacin kaddamar da kwamitin, Gwamnan Jihar Neja, Abubakar Sani Bello ya bai wa al’ummar jihar tabbacin cewa gwamnatinsa a shirye take wajen kare rayukan al’umma tare da bin hanyoyin da suka dace wajen mutunta kowani Dan’adam ba tare da nuna bambancin kabila ko addini ba.

 

Exit mobile version