Babban Sakataren kasuwar Mile 12 dake birnin Legas, Alhaji Idiris Balarabe Legas, kuma shugaban kwamitin gudanar da ziyarce-ziyarce a wadansu jihohin Arewacin Nijeriya, wanda Babban shugaban kasuwar ta mile I2, Alhaji Shehu Usman Jibirin Samfam Dallatun Abeokuta, kuma wakilin neman zaman lafiya a Jihar ogun, ya kaddamar da su, kuma ya turo su daga Legas zuwa Arewacin Nijeriya a matsayin wakilan kasuwar ta mile I2, da za su bi wadansu jihohin Arewa da suka shahara wajen noman kayan miya da sauran kayan abinci, sannan kuma suke kawo wa Legas domin saida wa a kasuwar ta mile I2 su jajanta wa manoma bisa asarar da suka tafka a bana sanadiyyar ambaliyar ruwa da kuma ‘yan ta’adda tare da ‘yan Boko Haram.
Babban sakataren kasuwar mile I2, Alhaji Idiris Balarabe ya yi addu’ar fatan Allah ya jikan wadanda suka rasa rayukansu da gafara, Allah ya sanya Aljanna ce makomarsu su kuma wadanda suka yi asara abisa wannan al’amari Allah ya mayar masu da alheri.
Ya cigaba da cewa, Alhamdulillahi a wannan zagaye sun samu nasarori masu yawan gaske inda suka fara ganawa da manoma da masu kasuwancin kayan miya da sauran kayan abinci na jihohin Sokoto Kebbi da Zamfara dangane da isar da wannan sako na shugaban kasuwar Alhaji shehu Usman Jibirin Samfam garesu, kuma manoman sun yi farin ciki da godiya game da lamarin.
Sannan su ma manoman suka cigaba da isar da sakon korafe korafensu tare da neman taimako ta yadda za su cigaba da bunkasa harkokin noma da kasuwan cinsu da sauran kayan abinci à kasuwar, da Nijeriya baki daya, ya kara da cewa sun dawo Jihar Kano inda anan ma suka zauna da manoman Kano, Katsina da Maiduguri, inda a nan ma suka gudanar da irin wadannan bayanai, nan take suka nuna farin cikinsu suka yi godiya sannan suka isar da sakonsu ga Babban sakataren kasuwar ta mile I2, domin ya isar da shi a wajen shugaban kasuwar Alhaji Shehu Usman Jibirin Samfam.
Shugabannin Kwamitin su ne; Babban Sakataren kasuwar Alhaji Idiris Balarabe Legas a matsayin shugaban kwamitin gudanarwa, sai ma’ajin kasuwar Alhaji sa’idu Usaini sarina, sai kuma sakataren kwamitin, Alhaji Mohammed Abdu kudan. Sauran sun hada da shugaban ciyamomin bangarorin kasuwar Alhaji Abdullahi Tukur kura da Shugaban bangaren masu sayar da Karas da Kabeji, Alhaji Bala yaro hunkuyi, da shugaban kulawa da cigaban kasuwan cin tumatir Alhaji Abdulgiyasu Sani Rano. Sauran su ne Shugaban walwala da jin dadin jama’a na kasuwar Alhaji Dauda Suleman, tare da shugaban bangaren dankalin turawa Alhaji kabiru tmk, da shugaban bangaren busasshen barkono Alhaji Muntari Jabo, sai shugaba mai kulawa da kasuwancin shinkafa, Masara Fawa da sauransu.