CRI Hausa" />

Kwamitin Kolin JKS Ya Fitar Da Shawarar Tsara Sabbin Shirye-Shiryen Bunkasa Kasar Sin

A tsakanin ranakun 26 da 29 ga watan nan, an shirya cikakken zama na biyar na kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin JKS na 19, inda mahalarta suka saurari wani rahoton da babban sakataren kwamitin kolin Xi Jinping ya bayar game da ayyukan da kwamitin kolin ya yi cikin shekara daya da ta gabata, sannan suka dudduba da kuma zartas da “shawarar kwamitin kolin JKS game da tsarawa, da kuma fitar da shiri na tsawon shekaru 5 na bunkasa kasar Sin karo na 14, da babban burin da ake son cimmawa zuwa shekarar 2035”.

A yayin taron, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi bayani kan shawarar filla filla.
A nan kasar Sin, “shirin bunkasa kasar Sin na shekaru biyar-biyar” ya kasance kamar wata muhimmiyar hanya ce da jam’iyyar JKS take bi wajen mulkin kasa, da kuma tafiyar da harkokin bunkasa kasar, ta yadda hakan zai zama wani muhimmin abu dake alamta yadda kasar Sin take samun ci gaba. A shekarar 1953, kasar Sin ta fitar da “shirin bunkasa kasar Sin na shekaru biyar” a karo na farko. Kawo yanzu, karo na 14 ke nan ana tsara sabon shirin bunkasa kasar na tsawon shekaru biyar masu zuwa. Bisa wadannan shirye-shirye na neman bunkasuwa na shekaru biyar-biyar, kasar Sin ta samu ci gaba kamar yadda ake fata.
A ganin Mr. Yao Jingyuan, wani shehun malamin dake aiki a hukumar ba da shawara ga majalisar gudanarwar kasar Sin, idan an kwatanta sauran shirye-shiryen neman bunkasuwa na shekaru biyar-biyar da aka tsarawa a da, a lokacin da ake aiwatar da sabon shirin bunkasar kasar Sin na shekaru biyar masu zuwa, kasar Sin ta riga ta zama wata mai zaman al’umma dake da matsakaicin karfi. Sakamakon haka, a cikin shekaru biyar masu zuwa, kasar Sin za ta kara mai da hankali kan yadda za a bunkasa tattalin arziki mai inganci, ba tare da matsalar hada hadar kudi ba.
“A lokacin da muke aiwatar da ‘shirin bunkasa kasar Sin na shekaru biyar karo na 13’, mu kan jaddada tabbatar da ganin tattalin arziki ya samu karuwa cikin sauri. Amma a cikin ‘shawarar tsara shirin bunkasa kasar Sin na shekaru biyar karo na 14’, an fi jaddada raya tattalin arziki mai inganci ba tare da tangarda ba kamar yadda ake fata. Wannan ya alamta cewa, yanzu mun fi mai da hankali kan ingancin tattalin arzikinmu, maimakon saurin karuwarsa kawai.”
Sannan bisa “shawarar kwamitin kolin JKS”, a cikin shekaru biyar masu zuwa, kasar Sin za ta fi mai da hankali kan kirkiro sabbin fasahohin zamani bisa ilmin kimiyyar zamani. A yayin cikakken zama na biyar, na kwamitin kolin JKS da aka rufe jiya, an gabatar da shawara cewa, a lokacin da ake aiwatar da “shirin bunkasa kasar Sin na shekaru biyar na 14”, dole ne a cimma burin inganta karfin kasa na kirkiro sabbin abubuwa bisa ilmin kimiyyar zamani, har ya ce, dole ne a tsaya kan matsayin sanya aikin kirkiro sabbin abubuwa bisa ilmin kimiyyar zamani, a matsayi mafi muhimmanci, domin zamanintar da kasar Sin. Dole ne kasar Sin ta dogora kan sabbin fasahohin zamani, bisa ilmin kimiyyar zamani da ta samu da kanta, a lokacin da take kokarin neman ci gaba.
Mr. Yao Jingyuan ya nuna cewa, “An fi bukatar kirkiro sabbin fasahohin zamani a lokacin da ake neman ci gaba mai inganci. Kasar Sin ta dade tana amfani da fasahohin zamani na sauran kasashe, domin neman ci gaba cikin sauri. Amma yanzu ta riga ta shiga lokacin neman ci gaba mai inganci, mai yiwuwa ne tattalin arzikinta zai kai matsayin sahun gaba a duk duniya. Sabili da haka, kirkiro sabbin fasahohin zamani ya zama abu mai muhimmanci matuka. Bugu da kari, a sanin kowa ne, tsirarun kasashe, da wasu ’yan siyasa, suna yunkurin hana mu samun fasahohin zamani domin hana ci gaban kasarmu. Sabo da haka, a cikin wannan sabon ‘shirin bunkasa kasar Sin na shekaru biyar’, an fi jaddada kirkiro sabbin fasahohi na zamani da kanmu.”
Bisa “tunanin sanya moriyar jama’a a gaban komai” wanda kwamitin kolin JKS dake karkashin jagorancin Xi Jinping yake da shi, a lokacin da hukumomin gwamnatin kasar Sin ta fara tsara wannan sabon shirin bunkasa kasar Sin na shekaru biyar, a karo na farko ta yi kokarin neman samun ra’ayoyin al’ummun kasar ta kafofin intanet, domin sanin abubuwan da suke jawo hankulan jama’a fararen hula. Sinawa daga bangarori daban daban sun gabatar da ra’ayoyinsu fiye da miliyan 1.
Game da wannan, Yao Jingyuan ya nuna cewa, dalilin da ya sa muke son neman bunkasuwa mai inganci a cikin shekaru biyar masu zuwa shi ne, jama’a fararen hula za su iya cin karin gajiyar bunkasuwar kasar. Mr. Yao yana mai cewa, “Makasudin tsara ‘shirin bunkasa kasar Sin na shekaru biyar masu zuwa karo na 14’ shi ne, tabbatar da ganin jama’a fararen hula sun ci karin gajiya, da kuma biyan karin bukatunsu na kara kyautata zaman rayuwarsu. A cikin sabon shirin, an fi mai da hankali kan batutuwan kula da tsofaffi, da samar da gidajen kwana masu inganci, da kuma kare ingancin muhallansu da dai makamatansu.” (Sanusi Chen)

Exit mobile version