Daga Wakilinmu.
A ranar Larabar da ta gabata ne Kwamitin Tallafatawa Marayu na Abuja karkashin jagorancin Sheikh Saidu Musa Yelwa na Kungiyar Izala wato JIBWIS ta raba wa ‘yan gudun hijira dake sansanoni daban-daban a yankin Abuja shinkafa fiye da buhuna 500.
Shinkafar wadda wani bawan Allah ya kawo a matsayin gudumawarsa ga dubban ‘yan gudun hijirar da rigingimu su ka raba da muhallansu dake fama da wahalhalun rayuwa, an sauke su a Babban Masallacin Juma’a na Shelkwatar Kungiyar Izala dake Utako a birnin tarayya Abuja.
Babban Limamin Masallacin, Imam Abdullahi Umar Adam ne ya jagoranci kwamitin zuwa rabon shinkafar ga ‘yan gudun hijirar da suka hada da Apo, Wasaa, Durmi, Waru, Maleshiya Estate Apo Billege da sauransu, inda daruruwan ‘yan gudun hijirar ke rarrabe a kwangwaye da bacoci mafi yawansu mata da yara kanana.
A yayin da yake zantawa da wakilinmu, Imam Abdullahi Umar ya bayyana cewa wannan wata sadaka ce da wani bawan Allah ya aiko, inda ya bukaci a mika ta ga ‘yan gudun hijira wadanda ya ce ya samu labarin irin wahalar da su ke fama da ita. “Wannan wata sadaka ce da wani bawan Allah ya aiko, don a rabawa ‘yan gudun hijirar da suke nan kewayen Abuja, kuma ba wannan ne karon farko da ya aiko irin wannan tallafi ba, a bara ma ya aiko da cikin tirela guda, sannan ya ce amana ce a garemu da mu sada ta zuwa ga wadannan bayin Allah dake cikin bukatu. A yau kamar yadda ku ke gani mun raba sama da buhuna 300, sannan kuma gobe idan Allah Ya kaimu zamu karasa ragowar rabon ga mabukatan,” a cewarsa.
Haka kuma malamin ya kara da cewa, wannan wani bangare ne na shirin Kungiyar Izala don tallafawa marayu da ‘yan gudun hijiran, wadda kimanin wata guda kenan mu ka gabatar da irin wannan tallafi a wannan masallaci ga daruruwan marayu da mabukata. Sannan sai ya yi kira ga Attajirai da su rika yin koyi da irin wadannan bayin Allah wajen tallafawa mabukata a fadin kasar nan, musamman ma marayu, zawarawa da ‘yan gudun hijira.