Sulaiman Bala Idris" />

Kwamitin PSC Ya Roki NLC Ta Janye Batun Yajin Aiki

Kwamitin tallafa wa shugaban kasa (PSC) ya roki uwar kungiyar kwadago da ta duba maslahar Nijeriya ta janye yajin aikin da ta ke shirin shiga.

Kwamitin ya ce, wannan yajin aikin da kungiyar ta kwadgo ke shirin shiga dangane da rashin zartas da mafi karancin albashi ba zai haifarwa da kasar da mai ido ba a irin wannan lokacin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ke tashi fadi wurin ganin ya daidaita lamurran tattalin arzikin kasa da walwalar al’umma.

Wannan rokon ya fito ne a wata takardar manema labarai da Daraktan Sadarwa da tsare-tsare na PSC, Mallam Gidado Ibrahim ya fitar a jiya, inda ya ce, ‘yan Nijeriya sam ba za su ji dadin wannan yajin aiki ba.

Mallam Ibrahim ya roki shugabannin kungiyar na kwadago da su yi la’akari da irin tsare-tsaren da gwamnatin Buhari ke da su kan inganta harkar tattalin arziki.

Ya ce, “mu na sane cewa, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari bai yi kasa a gwiwa ba wurin ganin an zartas da fara aiki da mafi karancin albashi, saboda ko ba komai ai shi ne ya fara shirin. Kowa shaida ne akan yadda shugaban kasar ya sanar da gwamnoni da su je su fara biyan wannan mafi karancin albashi.

“Kuma shugaban kasa Buhari ne ya fara tayar da batun cewa dole ne a tabbatar da an biya ma’aikata albashinsu. Inda har ma ya rika ba gwmanonin jihohi kudade don dai a tabbatar da fara aiki da mafi karancin albashin.

“Akan wannan ne ma ya sa Shugaba Buharin ya turawa da majalisar tarayya dokar da yake bukatar a gaggauta zartaswa. Babu wani abu da ya dauke hankalinsa a kan wannan, komi yana binsa ne a tsanake don ganin an kai ga nasara,” in ji kwamitin.

Kwamitin na PSC ya kara jaddada cewa, gwamnatin Buhari ba za ta zama kamar gwamnatocin bay aba, wadanda suka samu duk wani iko na iya biyan albashi, amma suka yi ta kin biyan ma’aikata hakkokinsu.

“Su gwamnatocin baya sun samu kudin, amma maimakon su kyautata rayuwar ma’aikata da ‘yan Nijeriya, sai kawai suka buge da almundahana da babakere. Amma a wannan karon, da yardarm Allah, Shugaban Kasa Buhari zai tabbatar da an fara biyan wannan mafi karancin albashi, a nan kusa ba da jimawa ba. Kuma kamar yadda muke ta fadi ne a baya, wannan gwamnatin tuni ta karya lagon cin hanci da rashawa a kasar nan,” in ji Mallam Gidado.

Exit mobile version