Kwamitin Shura na Jihar Kano, ya dakatar da Malam Lawan Shuaibu Triumph daga yin wa’azi a jihar.
Sakataren kwamitin, Alhaji Shehu Wada Sagagi ne, ya bayyana hakan a taron manema labarai da aka gudanar a yau Laraba a Kano.
- NAPTIP Ta Kama Mutum 5 Da Ake Zargi Da Safarar Mutane A Filin Jirgin Saman Abuja, Ta Ceto Mutane 24
- Nijeriya Za Ta Fara Ɗaukar Mataki Kan ‘Yan Ƙasashen Ƙetare Da Bizarsu Ta Ƙare
“Mun sake yin zama a yau, kuma mun duba ƙorafe-ƙorafen na sauti da bidiyo da aka turo. Za mu bai wa Malam Lawan Triumph dama ya zo ya kare kansa,” in ji shi.
Ya ce dakatarwar ta zama dole domin Malam Lawan ya samu damar zuwa gaban kwamitin ya kare kansa kan zarge-zargen yin kalaman da ake ganin na ɓatanci ne ga Manzon Allah (SAW).
Sagagi ya ce har sai an kammala bincike da jin bayanin Malam Lawan ne za a yanke hukunci na gaba.
Ya kuma yi gargaɗi ga ‘yan siyasa da su guji tsoma baki a lamarin, inda ya jaddada cewa a bar kwamitin ta kammala aikinsa cikin gaskiya da adalci.