CRI Hausa">

Kwamitin Tsakiya Na JKS Ya Fitar Da Takardar Farko Ta Ingiza Farfadowar Kauyukan Kasa

Yau Lahadi kwamitin tsakiya na jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin ya fitar da takardar farko ta shekarar 2021 a hukumance, inda aka bayyana cewa, kasar Sin za ta ingiza farfadowar kauyuka ta hanyar hanzarta zamanintar da aikin gona a fadin kasar daga dukkan fannoni. Wannan karo na 18 ne da kwamitin tsakiya na JKS ya fitar da takarda ta lamba ta farko domin ba da jagora kan aikin dake shafar kauye da aikin gona da kuma manoma, lamarin da ya nuna cewa, kwamitin tsakiya na JKS yana ba da muhimmanci matuka kan aikin a sabon zamanin da ake ciki.

A yayin da ake gudanar da shirin raya kasa bisa shekaru biyar biyar na 13 a nan kasar Sin, an samu babban ci gaba wajen gudanar da aikin gona na zamani, adadin hatsin da aka samu a cikin ‘yan shekarun da suka gabata ya dinga karuwa da sama da kilo triliyan dubu 65 a ko wace shekara, kuma matsakaicin adadin kudin shigar manoman kasar ya karu har ninki daya idan aka kwatanta da na shekarar 2010, kana an cimma burin kawar da talauci cikin nasara, yanzu haka ana gudanar da kwaskwarima a kauyukan kasar, har ma an samu sabon ci gaba, duk wadannan suna taka rawa ga ci gaban tattalin arzikin kasar.
Takardar farkon ta nuna cewa, yayin da ake kokarin aiwatar da shirin raya kasa na shekaru biyar biyar karo na 14, ana kokarin farfado da al’ummun kasar, da kauyukan kasar, a don haka kwamitin tsakiya na JKS yana ganin cewa, a sobon zamanin da ake ciki, aikin dake shafar kauye da aikin gona da kuma manoma yana da muhimmanci matuka, dole ne a kara mai da hankali kansa, ta yadda za a samar da wadata ga manoma.(Mai fassarawa: Jamila daga CRI Hausa)

Exit mobile version