Kwamitin Tsaro Na Majalisar Dinkin Duniya Ya Dauki Matakin Kawo Karshen Rikicin Libya

Kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya da yammacin ranar Laraba ta dauki sabbin matakai wajen magance rikicin da yaki ci yaki cinyewa na kasar Libya wanda hakan ya salwantar da dubban rayukan al’umma.

Hukumar lafiya ta duniya, WHO a rahoton da ta fitar ta ce; wadanda suka rasa ransu sun kai mutum 2, 280, wanda ciki mayaka 2, 000 suka rasa ransu, a yayin da fararen hula 280 suka rasa ransu har zuwa tsakiyar watan Janairu.

Wannan mataki da kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya ta dauka na zuwa ne makonni kadan bayan zaman yarjejeniyar sulhu ta mutum sha biyar da Birtaniya ta nema inda mutum sha hudu suka kada kuri’a a yayin da Rasha ta ki.

Daga cikin matakan da za a dauka harda gudanar da atisayen bai daya daga waje wajen tabbatar da an tsagaita wuta a Libya, tare da ganin kowanne bangare sun ajiye makamansu domin magance rikicin.

Exit mobile version