Connect with us

LABARAI

Kwamitin Yaki Da Korona A Gombe Na Ci Gaba Da Amsar Tallafi

Published

on

A kokarin da bangarori da kungiyoyi ke ci gaba da yi domin dafa wa yunkurin gwamnati na yaki da cutar Koronabairos a jihar Gombe, kwamitin yaki da cutar na ci gaba da samun karin tallafi daga sassa daban-daban.
Ko a shekaran jiya mataimakin gwamnan babban bankin kasa (CBN) Mista Edward L. Adamu ya tallafa wa jihar Gombe da sinadarin wanke hannu guda 1,500, abin rufe hanci da baki 100, da kuma sauran kayyakin kariya daga cutar Korona guda 100.
A wani wasikar da ya aike wa kwamitin yaki da cutar, Edward Adamu, ya ce ya bada tallafin ne domin shi ma ya taimaka wa yunkurin gwamnatin jihar na yaki da cutar, kamar yadda wata sanarwar da Ismaila Uba Misilli Kakakin gwamnan Gombe ya fitar a jiya ta shaida.
“Domin dakile ci-gaba da yacuwar annobar Korona a jihar Gombe da Nijeriya baki daya, ya zama wajibi ga kowa ya hada hanu tare da taimaka wa gwamnati domin tabbatar da yaki da cutar ta kowace hanya,” A cewar shi.
A wani makamancin wannan, shi ma tsohon dan majalisar wakilai na tarayya, Hon. Ali Isa JC ya mika tallafin naira miliyan daya wa kwamitin yaki da cutar Korona a jihar.
Hon. Ali JC wanda ya wakilici mazabar Balanga/ Billiri a majalisar wakilai ta kasa, ya ce tallafin kudin da ya bayar yayi ne domin taimaka wa gwamnati wajen yaki da cutar a jihar.
Da yake karban tallafin, shugaban kwamitin yaki da cutar, Farfesa Idris Muhammad ya gode wa wadanda suka bada wannan tallafi, yana mai cewa hakan zai taimaka gaya wajen marawa yaki da cutuka masu yaduwa baya a jihar.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: