Babban abinda ya damu Mati ba kamar karatowar damina. Na farko dai gidansa, gidan kasa ne, na biyu tsohon gida ne ya yi kasa sosai. Kusan za a iya cewa duk gidajen dake layin gidan Mati ya fi kowane yin kasa. Ba wannan ne kawai abin damuwa ga Mati ba, babban abin damuwar shi ne ba su da hanyar ruwa. Yana zaune a kofar gida shi kadai ya yi tagumi. Shi kadai ne kuma ba abokan hira. Jin rugugin iska ne ma ya farkar da shi, ya dubi inda ya ji karar ya ga ashe guguwa ce ta turnuke sararin sama. Ya tsahi da sauri ya nufi cikin gida. Koda ya shiga cikin gida ya iske matarsa a tsaye ita ma hankalinta a tashe.
“Maigida ni fa yau hankalina ba a kwance yake ba. Matukar wannan ruwa ya saukam gidan nan ambaliya zai yi. Gara ma kawai mu fara tattara duk wani kaya da zai iya jikewa”
“Ai ba wannan ne abin damuwa ba, kin san gidan ya tsufa, da an ce ruwa ya yi ambaliya zai iya rusa gidan ta kasa” Mati ya cewa matarsa
“To, Allah dai ya kiyaye. Ni dai bari in fara tattara kayan” matarsa ta ce ta kuma yi kiran diyansa mata suka fara tayata tattara kaya.
Kafin ka ce ga farin zare, gari ya yi duhu guguwa mai karfi ta taso, sai gunji take yi da wani fito-fito. Hantar cikin Mati ta kada ta kara kadawa, ya shiga addu’o’i. Aka fara yayyafi.
“To, mu dai yau, Allah ga mu gareka sai kuma yadda ka yi da mu” ya cewa kansa. Sai kawai ya ji yayyafin ya dauke. Kafin wani lokaci, gari ya washe. Wannan hali da Mati ya shiga yau, haka ya sake shiga kashe gari. Duk da cewa ba shi kadai ne hankalinsa a tashe ba a wannan unguwa ta su, saboda tararrabin rashin magudanar ruwa, Mati ya fi kowa tashin hankali saboda yadda gidansa yake.
Mati na daya daga cikin manyan ‘yan siyasa da ake ji da su a wannan unguwa tasu. Hasali ma, shi jami’I ne na jam’iyya, kuma kowane irin kulli da kwancewa da su ake yi. Su ne suka tashi tsaye, suka dage wurin ganin an zabi shugaban Karamar Hukumarsu da kuma Kansilansu.
Babu shakka ba karamar rawa ya taka wurin yin magudi da almundahana wurin ganin cewar su wadanda ke ci yanzu sun hau. Ya samu ‘yan kudi a lokacin da ake ta hada-hadar. Mati ya tabbatar da cewa su wadannan mutane da ya dage akan sai an zabe su ba su cancanta ba, amma a cewarsa, su hannayensu a bube suke. Ba za su zabi dan boko ba.
Yau dai ta rutsa da Mati, domin kuwa, ruwan sama ya goce yau da magariba kamar da bakin kwarya. Gari ya cika da ruwa, kusan in ka shigo wannan unguwa sai ka dauka a cikin wani kududdufi kake. Da Mati da matarsa da kuma diyansa gaba daya a tasye suka kwana, gidan ya cika da ruwa ya yi makil. Haka suka yi ta addu’o’I har gari ya waye. Bayan an kira assalatu ne Mati ya samu ya fita daga gidan ya wuce masallaci. Koda ya dawo daga masallaci ya iske zauren gidansa ya zame ya ruguzo. Babbar sa’arsa ita ce, iyalinsa sun samu sun fita babu wanda ya yi rauni.
Da hantsi aka yi ta zuwa ana yi masa jaje. Suna nan zaune kofar gida ana jaje aka kuma shiga hirar duniya. Ana cikin hira ne sai ga Malam Hudu ya zo yi wa mati jaje. Malam Hudu dai shi ne kansilan da ya tsaya takara da mai ci yanzu, wanda su Malam Mati suka yi kutun-kutun suka hana takara. Bayan ya yi jajensa ya tafi ne wani daga cikin abokan Mati ya ce “Amma dai mun ji kunya wallahi”
“Kunyar me kuma?” wani daga cikin abokan ya tambaya.
“Ganin har Malam Hudu ya zo ya yi mana jaje amma ban ga honorabul ba”
“Ai zai zo, ka sa ranka a inuwa” Mati ya ce.
Aka dai ci gaba da tattauna al’amuran siyasa. Yau kwanaki uku da rushewar zauren Mati Honorabul Kansila bai zo ba, tun Mati na kyautata zato har abin ya fara damunsa.
“Wai Honorabul bai san abinda ya same ni ba ne?” ya tambayi kansa
“Ya sani mana, ai na aika masa, har chiyaman ma na aika kuma an dawo an gaya mani cewa an gaya musu har sun ce a yi mani jaje kafin su zo…” ya fara ba kansa amsa
Matarsa ta leko ta ce “Malam kai da wa kake magana ne?”
“Wallahi ni kadai ke magana, gani na yi har yanzu yaron nan bai zo ya yi mani jaje ba”
“Wane yaro fa” ta tambaya
“Kansila mana”
“Oho, ai honorabul za ka ce” ta gayara masa.
“Ya yi shiru bai ba ta amsa ba, ita kuma ba ta kara ce masa kanzil ba. Ta ma koma ta ci gaba da ayyukan da take yi. Kofar gida dai an samu ‘yan tsofaffin kwanuka an kare.
Mati dai yana nan tsakar gida zaune yana kulla wannan ya kwance wancan. Sai ya ji sallama daga kofar gida. Ya amsa sallam ya fita. Abokin siyarsa sa ne Kwamared ya zo yi masa jaje.
“Malam ashe haka abu ya faru?”
“Wallahi”
“To Allah ya kiyaye gaba. In ji dai ba wanda ya yi rauni?”
“A’a ba kowa wallahi”
“To Allah ya kiyaye gaba. Ni zan koma”
“To na gode, Allah ya saka da alheri, na gode” inji Mati har ma da dan takawa Kwamared.
Mati na komawa cikin gida sai ya ji ana labaran duniya. Ya kuwa koma gefe yana sauraro “Jama’ar karamar hukumar DYZ sun zo wannan gidan Radiyo domin yin godiya ga shugaban karamar hukumarsu saboda abinda suka kira –ceto rayukansu da yayi a wannan damuna, Alhaji Mamman Ya’u wanda ya wakilci mutanen unguwar Zabeb kirki ya yi karin bayani kamar haka ‘wallahi mu dai mun gode masa da hanyoyin ruwa da ya yi mana, ba don haka ba da damunar bana ta yi gyara….’” Aka dauke wutar lantarki. Wannan ne ya katse labaran da Mati ke ji. Ya yi tsaki.
“Kai da wa kuma?” matarsa ta tambaya
“Kin dauka da NEPA nake ko” ya ce mata
“Dama mana, sun hana ka jin labaran chiyamomi na gaskiya”
“Me kike nufi da chiyamomi na gaskiya?”
“A, na gaskiya mana, mu da kuka yi mana zaben tumun dare ba gashi an bar mu ba hanyar ruwan ba, sai rusassun zauruka da dakuna”
Wannan magana ta maidakin Mati ta ratsa shi. Ya yi shiru bai ce mata komai ba. Ya ce a ransa “Ashe mata ma sun san mun yi ba dai-dai ba?”
“Maigida ba ka ce komai ba” ta ce masa
“To me zan ce, ai aikin gama ya gama, ni bari ma in shiga bandaki” ya ce ya tashi ya dauki buta ya zagaya. Mati ba wani abu ya kai shi bandaki ba illa dai ya je ya zauna ya yi nazarin maganar da matarsa ta kafta masa ba tare da wani ya katse masa tunanin ba. Ya tsuguna ya shiga tunanin maganar matarsa. Wannan ne ya sa ma ya tuna wata takaddama da suka yi da su Kwamared daf da za a yi zabe. Yana tuna abin ne kamar wani majigi…..
Nalado ya dubi Mati cike dsa mamaki ya ce masa “haba Mati, a ce mutum bai da wata magana sai ta kudi”?
“Kwandala ita ce komai mutumina, ina dai tabbartar maka dacewa matukar Alhaji Mai wayo zai fitar da tsari babu abinda zai hana mu tsaya muga ya kada Hudu Malam Hannu rufe”
“To ai Malam Hudu yafi mai cancata in dai cancanta za’a duba” Nalado ya maida martani
“Nalado, mu cancanta bata wuce Naira ba, shin me kake jin zamu samu in muka ce sai zaben cancanta . Mun sani malam Hudu ya fi cancanta don yafi amana da dattako da ma kwarewa a fuskar aiki, amma matsalarsa guda ita ce ba zai kula da ‘yan siyasa ba, kuma ya cika taurin kan tsiya, inji Mati.
“In dai zai yi aiki ai babu komai, ai ba lalle ne sai ya baiwa ‘yan siyasa wani abu ba, ai mu a matsayinmu na ‘yan siyasa talakawa muke yiwa aiki” inji Nalado.
Mati ya goce da wata dariya mai nuna cewa har yanzu Nalado cikin loko yake bai fito fili ba. “Haba malam wa ya ce maka talakawa muke yiw aiki” mu kanmu muke yiwa aiki, matukar baza mu samu komai ba, ba ruwanmu da duk wani aiki da za’a yiwa talaka.
“Amma abin naku da daure kai. To bari kaji abinda yasa na damu Alhaji mai wayo mutum ne mai zari hadama da kuma rashin tausayi, ka manta bubuwan d yayi a baya. Shekaru hudu yayi yana shugabancin karamar hukuma amma me yayi mana banda barnar bdukiya jama’a da zalunci, ace har yanzu ko hanyar ruwa bamu da ita, da zarar anyi rywn sama mun shiga zullumi ke nan, kuma a haka sai yace yana son tazarce? Ai bashima da kunya.
“Kai dai naga alama baka fahimci inda aka sa gaba ba a kasar nan ba, kaga deliget ne zasu yi zaben nan. Da zarar ya fitar da tsari muka zaga muka ba kowa dubu goma wallahi magana ta kare yunwa ce ke damunsu ba cigaba ba, inji Mati.
“To Allah ya sauwake mana wannan hali da muka shiga don abin da ban tsoro.uwar zamu tafi ahaka mun gma yawo, inji Nalado
“Salamu alikum’ inji wata murya mai kauri
“Suka amsa masa sallama”
“Kwamared ne a gari” inji Mati
“Nine Allah ya kawo mu, kasan tun da zabe ya karato gara mu dawo gida mu wayar da kan jama’a.
“Amma anyi murna da jin haka” inji Nalado
“Ku da kuka ce ba ruwanku da siyasa sai boko, Mati yace cikin zullumi. Babu shakka bai ji dadin wannan magan ta kwomared ba domin yasan abinda shigowarsu zata haifar.
“To ai gani muku yi ai wadnda muka dora sun kasa, ban da zaden mutum dare babu abinda suke yi mana sai turin mota, kaga gara mu dawo mu karbi abinmu” Ya mayar
“Ashe kuwa” Mati ya tambaya.
“sosai” kwamared ya amsa cikin natsuwa
“ka ce dai kun zo kuyi mana juyin mulki kawai, watau kunga koyarwa babu ci kunzo ku kore mu?” Mati yace a fusace
“Ai ba maganar kora bace, maganar gaskiya ce ayita da wando Nalado yace Mati ya data rai, ya mike tsaye ya karkade rigarsa “Zan karasa majalisa don muna da mitin”
“Ban gane ba ka tsaya mu karasa maganar mu mana” Nalado ya ce
“Ma hadu anjima, sai anjima kwamared” ya ce ya juya abinsa yana ta sake sake a zuciyarsa.
“Mun shiga uku matukar wadannan ‘yan boko suka gano zaren siyasar, amma in sun san wata, ba su san wata ba ai” in ji Mati…
Kiran sallar la’asar ne ya katse masa wannan dogon tunani mai kama da mafarki da yake yi. Ya fito ya yi alwala ya tafi masallaci. Ana idar sa sallar ya wuce majalisa cikin zakuwa. Lallai yau rana ce da ake cewa ta wanka wadda ba a boyon cibi.
Koda ya isa wurin ya iske mutane biyu ne kawai, suka gaisa, aka ci gaba da hirar matsalar wuta. Shi Mati abinda ya kawo shi daban , amma ba ya son ya fadi komai sai majalisar ta dinke tukunna.
Suna cikin wannan hali ne Kansila ya zo ya wuce ta inda suke, ko kallowa bai yi ba, sai ma cin taya da ya yi wadda ta budesu da kura. Saukinsu ma kawai shi ne, garin damina ne. Wannan abu ya bata wa mati rai, ya kasa daurewa ya kunduma ashar. Aka tattaushe shi.
Lokacin da ya fara zage-zage kashi na biyu, majalisa ta riga ta dinke, kowa na da abin fada. “aiki banza, aikin wofi” Mati ya ci gaba.
“Haba Mati, kar ka raina mana wayo mana. Nan fa ka dage akan cewa ba ruwanka da yi wa talakawa aiki…” wani abokinsa ya mayar masa da martani.
“Na ji na fada, amma ai ba dai-dai ba ne wannan iskanci da suke yi mana, ai wulakanci ne”
“Assalamu Alaykum” wata murya da wasu suka yi murnar jinta a dai-dai wannan lokaci, kowa ya amsa masa sallama.
“Kwamared ka zo a dai-dai” in ji Nalado, abokin Mati. Mati ya dubi Nalado ya ce “kai dai ka cika fitina” kowa a wurin ya fashe da dariya domin fahimtar inda maganar Mati ta dosa.
“To, ranar wanka dai, Hausawa sun ce ba a boyon cibi, Kwamared maganar zaben tumun daren da aka yi mana ne ake yi, ka san an ce rana ba ta karya, wai sai dai uwar diya..:
Aka cika masa “ta ji kunya”
“To ai dama na gaya muku mu tsaya mu zabi mutane masu mutunci wadanda za su kula da hakkin kowa da kowa, nan su Mati suka yi kememe suka ce alabaran ba su san maganar ba. Aka zabe suka yi munamuna aka kada wadanda ya kamata a zaba.” Inji Kwamared.
“Ga shi an bar mu da rusassun soraye ba…Mati ina za ka kuma” Nalado ya ce da ya fuskanci Mati na kokarin tafiya.
“Gida za ni” ya ce cikin borin kunya
“Dawo Mati” in ji Kwamared
Mati ya dawo ya zauna. Aka shiga tattaunawa mai zurfi ta yadda sai da kowa ya amince da cewa duk wanda ya kira kansa dan siyasa, nauyin tsayawa a zabawa mutane shugabanni na gari ya hau kansa. “Duk wanda ya goyi bayan karya, ba kowa ya cuta ba kansa” Malam Idi, wani abokin Mati ya ce.
“Har kun tuna mun wakar Aliyu Dandawo inda yake cewa ‘Kowayyada gaskiya yaddau karya, yana sanin abin banza yayyi…’” Mati ya rero. Kowa ya fashe da dariya.
“Hausawa dai sun ce ‘Gaskiya daya ce, kuma daga kin gaskiya sai bata’” in ji kwamared.
“Allah ya sa mu gane” mutane biyu suka hada baki a cewa.