Kwankwaso Ne Gwaninmu A Babban Zaben 2019 – Magoya Baya

Daga Muhammad Shafi’u Saleh, Yola

Wasu daruruwan matasa magoya bayan tsohon gwamnan jihar Kano Dakta Rabiu Musa Kwankwaso, sun jaddada goyon bayansu da cewa shi ne gwaninsu a babban zaben 2019 da ke tafe.

Matasan da suka fito daga yankin arewacin jihar Adamawa, sun bayyana haka ne a wani taron neman goyon bayan jama’ar yankin da suka gudanar a garin Mubi, suka ce Kwankwaso suke bukata ya tsaya takarar shugabancin kasar.

Da ya ke jawabi a taron shugaban kungiyar magoya bayan Kwankwason a jihar Abubakar Muhammad Jada, ya ce Kwankwaso shi ne zabinsu a babban zabe mai zuwa, don haka suka taru domin neman goyon bayan jama’a.

Kwankwaso shi ne gwaninmu, shi ne dan takararmu a babban zaben 2019, shi muke fata saboda haka muka hadu domin neman goyon bayanku”.

Ya ce Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ne kawai dan siyasar da yake da manufa ingantacciya wajen bunkasa tattalin arziki da samar da ci gaba na siyasa, kasancewar yana kwarewa ta kowane fanni.

Alhaji Bamanga Tukur shi ne shugaban kungiyar a yankin kananan hukumomin Adamawa ta arewa, ya ce suna da dalillai da dama da yasa suka yarjema kansu cewa Kwankwaso shi ne jarumin da zai cire musu kitse a wuta, domin jajirtacce ne.

Ya ce bisa kwarewa da jajircewar Kwankwaso yasa ake mishi lakabi da Sanatan Arewa, yace babu wani abu da ya shafi jama’ar arewa da Nijeriya da Kwankwaso bai nuna damuwarsa akai, don haka suna da dalilai da dama na neman goyon bayan jama’a.

“Mun yi amanna Kwankwaso shi ne daya tilo da zai share mana hawaye, wannan ya sa kungiyarmu ta yi tsayin daka sai mun kai ga gaci, sai mun tabbatar mun shigar da Kwankwaso Aso Rock a 2019 insha Allahu.” In ji shi.

Exit mobile version