Kwankwaso Ya Jibge Mana Bashin Fiye Da Naira Biliyan 54 Kan Aikin Hanyoyi Na Kilomita 5 – Ganduje

Gwamnatin Kano

Daga Abdullahi Muhammad Sheka, Kano

 

Gwamnatin Jihar Kano a karkashin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ta bayyana cewa, tsohuwar Gwamnatin Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso ta jibge mata bashin Naira Biliyan N54, 408, 259, 638.05 na aikin hanyyoyi masu tsawon kilomita biyar-biyar a fadin kananan hukumomin jihar 44.
Kwamishinan ma’aikatar yada labaran jihar Malam Muhammad Garba ne ya bayyana haka a lokacin taron manema labarai jim kadan da kammala taron majalisar zartarwar mako-mako da aka saba gudanarwa a dakin taro da ke fadar gwamnatin jihar.
Ya ce, Majalisar zartarwar ta karbi rahoton kwamitin kwararru wadanda suka duba aikin hanyoyin masu tsawon kilomita biyar-biyar wanda gwamnatin da ta gabata ta bayar da kwangilarsu karkashin rusasshiyar ma’aikatar kasa da tsare tsare wadda hukumar tsara karkara ta Jihar Kano (KNUPDA) ke duba aikinta.
Malam Garba ya ci gaba da cewa, kwamitin ya ziyarci kananan Hukumomi 39 inda aka tattaro bayanai kan kasafin kudin da aka bayar da kwangilar yin aikin, da halin da aikin yake ciki a yanzu, da matsayin aikin da aka aiwatar, da adadin kudin da kuma yawan kudin da aka fitar domin aikin.
Kwamishinan ya kuma nuna cewa, aikin hanya mai tsawon kilomita biyar-biyar a wasu kananan Hukumomi uku an kwace su sakamakon gaza tabuka komai a kananan hukumomin Ungogo da Dawakin Tofa, ya yin da wasu bangarorin aikin hanyar Tsanyawa da Bichi da ke kan titin Kano zuwa Katsina an bar wa ma’aikatar ayyuka da gidaje ta gwamnatin tarayya bisa bukatar hakan.
Ya ce, wasu ayyukan guda uku a kananan hukumomin Rimin Gado, karaye da Bunkure da suka fada cikin manyan hanyoin an karkatar da su tare da sake bayar dasu daban domin aiwatarwa, yayinda kananan hukumomin kwaryar birni da suka hada Dala, Nassarawa, Gwale, Birni da kewaye da Tarauni an cusa su a matsayin aikin hanya mai tsawon kilomita biyar-biyar.
Malam Garba ya kuma nuna cewa, majalisar zartarwa ta amince da kashe Naira Miliyan N607, 124, 663.47 don gyara hanyar Rimin Gado zuwa Sabon Fegi zuwa Jilli zuwa Gulu duk a yankin karamar Hukumar Rimin Gado.
Kwamishinan ya kuma bayyana cewa an samu amincewa majalisar zartarwa na mayar da makarantar unguwar zoma dake Gezawa zuwa matsayin makarantar horar da malam jinya ta Gezawa domin zama wurin horar da karin kwararrun unguwar zoma domin rage matsalar haihuwa da lura da kananan yara a Jihar Kano

 

Exit mobile version