Ibrahim Muhammad" />

Kwankwaso Ya Kaddamar Da Kwalejin Koyon Jinya A Garin Kwankwaso

A ranar Litinin ne tsohon Sanatan Kano ta tsakiya kuma tsohon Gwamnan Jihar Kano Madugun Kwankwasiyya ya bude makarantar Zamani ta koyon aikin Jinya da Unguwar zoma ta mata a garin Kwankwaso mahaifarsa dake cikin karamar hukumar Madobi.
Bude wannan kwalejin na koyon aikin jinya da Unguwar Zoma na daga cikin bukukuwan da Sanatan yake na cikarsa shekaru 63 a duniya. Dinbin jama’a ne daga sassa daban-daban a ciki da wajen jihar Kano suka halarci bude kwalejin.
Sanata Rabiu Musa Kwankwaso a jawabinsa ga dinbin jama’a da suka halarci bude kwalejin ya ce, ya yi amfani da wannan dama ne na cikarsa shekaru 63 ya gode wa Allah sannan maimakon buki ya yi wani abu da zai taigmaki cigaban rayuwar al’umma ta bude wannan kwaleji da za’a rika koya wa mata aikin jinya da unguwar zoma.
Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya ce, kwalejin zai soma da dalibai yan mata guda 50 wanda nan gaba za’a iya kara adadinsu. Bayan koyarda harkar jinya Kwalejin zata rika bai wa mata a yankunan kananan hukumomi horo akan karbar haihuwa da hakan zai taimaka a unguwanni da kauyukan jihar Kano.

Exit mobile version