Connect with us

LABARAI

Kwankwaso Ya Kai Wa Fayose Ziyara

Published

on

Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Rabi’u Kwankwaso, ya gana da Gwamnan Jihar Ekiti, Ayodele Fayose, a fadar gwamnatin Jihar da ke Ekiti, a ranar Litinin.
Duk da cewa, ba a bayyana ainihin abin da suka tattauna ba, amma dai mutanan biyu sun yi kira da a tabbatar da an yi zabe na gaskiya cikin lumana a zaben gwamnan Jihar da za a yi ranar 14 ga watan Yuli.
Cikin sanarwar manema labarai da mai magana da yawun gwamna Fayose, Mista Idowu Adelusi, ya fitar ya ce, Kwankwaso, wanda a yanzun haka dan Majalisar Dattawa ne a karkashin inuwar Jam’iyyar APC, ya kuma gana da al’ummar arewa mazauna Jihar.
Ya bukace su da su zauna lafiya da masu masaukinsu, su kuma tabbatar sun mori damarsu ta zabe kamar yadda tsarin mulki ya yarje masu.
Ya ce, bai kamata zabe ya zama lamarin ko a mutu ko a yi rai ba, amma dai a tabbatar da an yi adalci.
“Kwankwaso, ya kuma nu na tsananin damuwarsa kan yawaitan kashe-kashen da ke aukuwa a wasu sassan kasarnan, ya yi nu ni da cewa, hakki ne da ya hau kan gwamnati ta tsare rayuka da dukiyoyin ‘yan kasanta.
Da aka yi masa tambaya kan ko yana shirin yin watsi da Jam’iyyar ta APC ne ya koma ainihin Jam’iyyarsa ta PDP, sai tsohon Ministan tsaron ya ce, duk abin da ‘yan’uwansa na rusasshiyar sabuwar Jam’iyyar PDP, suka cimma matsaya a kansa, shi ne zai samar da makomar na shi a nan gaba.
Advertisement

labarai