Daga Mustapha Ibrahim Kano
Ɗaya daga cikin jagororin matasa `yan gaban goshin shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari tun da ya fito neman Shugabancin Ƙasa a tsohuwar Jam`iyyar ANPP da CPC da kuma Jam`iyyar APC wanda a cikin ta haƙarsu ta cimma ruwa.
Ambasada Ali Barakat ya bayyana cewa, Sanata Rabi`u Musa Kwankwaso, Tsohon gwamanan Kano ya yaudari shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari da ayyuka da ke cike da son zuciya. Barakat ya bayyana haka ne cikin wata hira da ya yi da wata kafar yaɗa labarai mai zaman kanta a makon da ya gabata a Birnin Kano.
Ali Barakat wanda ya bayyana cewa lokacin da suka kawo wa Muhammadu Rabi`u Musa Kwankwaso ziyara gidan gwamnati, ƙarƙashin Jagorancin Muhammadu Buhari basu san ayyukan da gwamnan ya yi na son zuciya ba ne, sai yanzu da suka samu bayanai dalla-dalla a rubuce irin aringizo da son zuciya da tsohon gwamnan Kanon ya yi a wancan lokacin, don haka yanzu sun shata layi da Sanata kuma yana mamakin yadda matasa suke son Kwankwaso kawai don dai basu sanshi ba ne, a cewar Ali Barakat.
Haka kuma ya ce, Ayyukan da tsohon Gwamnan ya ɗebo a ƙananan hukumomi 44 na gina hanyoyi kilomita biyar a kowacce ƙaramar hukuma ba a yi komai ba, amma ya kwashe kaso mai tsoka a aikin da ya bayar haka aikin Gina makarantun nazarin harshen larabci da Addinin Musulunci shi ma aikin bai yi nisa ba amma Sanata Rabi`u Musa ya kwashi kaso mai tsoka a kuɗin.
Ya dai bayyana cewa akwai maƙudan kuɗaɗe da ya yi awon gaba da su da sunan ya yi aiki saboda haka duk wata Badaƙala yanzu Buhari ya na da cikakken bayani.
Daga ƙarshe Barakat ya yi shelar cewa, ko da ma Buhari bai yi niyyar takara ba a 2019 za su tilasta masa ya yi takara kamar yadda suka yi a baya, don ya ɗora akan inda ya tsaya na gyaran Nijeriya, kuma ya ce bai kamata Kwankwaso ya matsu da sai ya zama shugaban ƙasa ba a wannan lokaci, ya jira tukunna har lokacinsa.