Daga Ibrahim Muhammad,
Tsohon Gwamnan jihar Kano, Sanata Injiniya Dakta Rabiu Musa Kwankwaso ya tarbi dalibai guda 370 da suka kammala karatunsu a jami’oi daban-daban na kasashen duniya daya dauki nauyinsu a karkashin gidauniyar cigaban Kwankwasiya.
Da ya ke jawabi ga daliban bayan saukarsu a filin tashi da saukar jiragen sama na kasa da kasa na Malam Aminu Kano. Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya nuna matukar farin cikinsa da kammala karatun daliban da kuma samun kyakkyawan sakamako suka komo gida cikin koshin lafiya daga jami’oi daban-daban a kasashen Dubai, Indiya da Sudan.
Ya bayyana cewa wannan rana ce muhimmiya ta tahiri da mafarkinsa ya zama gaskiya kuma tayasu murna da farin ciki da dawowarsu gida lafiya.
Kwankwaso ya yi nuni da cewa sha’awarsa ga ilimi bashi da iyaka musamman ga ‘ya’yan talakawa, don tabbatar da tallafawa cigaban ilimin ya yi duk wani abu mai muhimmanci na samun nasarar tura daliban karatu da aka yi kasashen Waje.
Injiniya Dokta Rabiu Musa Kwankwaso ya ce, dukkan daliban da suka kammala karatun guda 370 a kasashen Indiya da Dubai da Sudan a fannoni daban daban an dauki dukkan dawainiyar karatunsu tun daga tafiyarsu har dawowa da masaukin
Shima a nasa jawabin shugaban dalibai da Gidauniyar Kwankwasiyyar ta turasu suka yi karatun suka kammala na banban digirin Digiri Yusif Baba Dala ya nuna farin cikinsa bisa wannan babban tagomashi na alkhairi da Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso ya yi musu na turasu karatun da suka sami canji a rayuwarsu.