Kwankwaso Zai Kauda Zaman Kashe Wando Idan Ya Samu Mulkin Basar Nan –Boss

An bayyana cewa idan Allah yasa jagoran Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya sami mulkin basar nan zai bai wa harkar ci gaban matasa kulawa dayakamata domin kawo ci gaba da bunbasar al’umma.
Jigo a jam’iyyar APC Kwankwasiyya a baramar hukumar Nasarawa kuma mai neman kujerar majalisar tarayya na yankin. Alhaji Muhammadu Aminu. wanda akafi sani da Alhaji Abba Boss ya bayyana hakan da yake zantawa da jaridar LEADERSHIP A Yau a wajen taron walima da baddamar da jagororin APC Kwankwasiyya na baramar hukumar Nasarawa da jagoran Kwankwasiyya na yankin, ma’ajin jam’iyyar APC na basa, Alhaji Bala Gwagwarwa ya jagoranta a ofishin jam’iyyar dake kan titin Yan’kaba a yammacin lahadin da ta gabata.
Alhaji Abba Boss ya bara da cewa matasa da mata sune Najeriya shi yasa shi yasa Sanata Rabiu Musa kawnkwaso idan zaiyi kira sai kaji ya ce, ‘Ina matasa! saboda su ne bashin bayan ci gaban basar nan.’
Yayi nuni da cewa zaman jagwam da yawancin matasa suke shi yake sawa suke abinda bai kamataba irinsu shaye-shaye da sauran abubuwa da basu dace da mutuntaka ba dan haka”Idan mai gidammu Kwankwaso ya hau mulkin Najeriya zamu maida hankali wajenmbaiwa matasa ayyukanda zasuyi, bawai na Gwamnati kona kamfani ba, za’a koyawa matasa da mata sana’oi na dogaro dakai wannan shine manufarmu kuma insha Allah wannan zaman kashe wando da ake a Najeriya sai mun kawo barshenta”. Abba Boss. Yayi bayanin cewa taken APC ne chanji, chanji kuma alheri. A cikin APC ma mu yan’kwankwasiyya ne, saboda haka in sun ce kwankwasiyya! Amana!.
“Mu ka ce daga Daura sai Madobi, daga Madobi sai bila, daga bila sai aiki daga aiki sai Aljanna. Abinda muke nufi daga Daura mulkin Najeriya take yanzu zata koma madobi daga madobi bila zamu tafi . Kwankwasone zai shiga bila idan aka shiga bila sai aiki sai aljanna, ba wanda bayaso ya shiga aljanna. Zamuyi aikin alkhairi saboda ci gaban mutane Allah zai saka mana da ladammu da aljanna”cewar Abba Boss.
Alhaji Muhammad Aminu Adamu Boss ya ce; taron waliman na farin cikine da bara hada kan yan’kwamkwasiyya a Nasarawa, dama haka suke uwa daya uba daya barbashin jagorar Nasarawa ma’ajin APC na basa.

Exit mobile version