Kwanton Bauna: Mun Nuna Wa Boko Haram Fin Karfi – Rundunar Soji

Mazauna Kauye

Rundunar sojojin Nijeriya ta ce, ta nuna wa kungiyar Boko Haram fi n karfi bayan da dakarunta su ka sake murkushe wani kwanton baunan da ’yan kungiyar ta Boko Haram su ka yi mu su a karamar hukumar Dikwa ta Jihar Borno.
Shugaban sashen yada labarai na rundunar Sojin, Kana7ntan baunan da sauran guggubin Boko Haram su ka yi mu su a kan hanyarsu a daidai kauyen Ala da ke da nisan kilomita bakwai da garin na Marte.
“Sun yi kwantan Baunan ne tare da shuka wa zaratan sojojin namu nakiyoyi da sauran ababe masu fashewa.
“Bayan namijin kokari, juriya, kishin kasa da nuna kwarewa, dakarun sojin sun komo bayan matsalar farko, su ka ragargaji ’yan ta’addar.
“Zarantan sojojin namu sun nuna mmm
n AK-47 guda uku da sunkin harsasansu guda shida da kuma babur din hawa samfurin AOJOE guda daya da kuma tufafin sawa, kayan abinci da kayan gyaran ababen hawa na ’yan Boko Haram.
A cewarsa, yawancin ‘yan ta’addar na Boko Haram sun gudu ne dauke da raunukan harbin bindiga a jikkunansu.
“A yanzun haka dakarunmu su na cigaba da kai komo a yankin domin hana ‘yan ta’addan sakat.
Babban hafsan dakarun kasa na kasar nan, Laftana Janar Tukur Buratai, ya yaba wa dakarun sojin a kan wannan namijin kokarin da su ka yi.
“Ya kuma mika godiyarsa ga dukkanin ’yan kasa nagari a kan goyon baya da fatan alherin da su ke yi wa sojojin a kokarin da sojojin ke yi na kawo karshen matsalolin tsaro da su ke fuskantar wannan kasar t&amu.”

Exit mobile version