Daga CRI Hausa
A kwanakin baya ne, Shugaban cibiyar nazarin muhimman manufofin kasashen Asiya dake kasar Panama Julio Villarres ya fidda wani sharhi mai taken “Gaskiyar batun hakkin dan Adam a kasar Sin” a jaridar Rebelion ta kasar Spain, inda ya ce, kasashen yammacin duniya suna da mummunan buri na bata sunan kasar Sin ta hanyar yada jita-jita game da batun hakkin dan Adam a kasar ta Sin, ya kuma jaddada cewa, kasar Sin ta ba da muhimmiyar gudummawa a fannin kare hakkin dan Adama a duniya.
Yana mai cewa, kasashen yammacin duniya suna yada karairayi marasa tushe domin bata sunan kasar Sin, amma, ba za su cimma burinsu ba, ya kuma nunawa duniya yadda ake keta hakkin dan Adam a kasar Amurka, inda mutane suke fama da matsalar yunwa, da rashin aikin yi, da rasa gidajen kwana, karancin kayayyakin kiwon lafiya, da kuma matsalar ra’ayin nuna wariyar launin fata da dai sauransu, wadanda suka haddasa tashe-tashen hankula a wannan kasa. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)