CRI Hausa" />

Kwararru Da Masanan Sin Suna Kira A Yaki Kalaman Nuna Kyama A Taron MDD

Taron MDD

An gudanar da taron dandalin tattauna batutuwan da suka shafi mutane marasa rinjaye na majalisar kula da hakkokin dan Adam ta Majalisar Dinkin Duniya karo na 13, daga ranar 19 zuwa 20 ga wata. Dandalin mai taken “Furucin nuna kyama, kafafen sada zumunta gami da mutane marasa rinjaye” ya samu halartar wasu kwararru da masana gami da wakilan kungiyoyin al’umma daban-daban na kasar Sin, inda suka gabatar da manufofi da ayyukan da gwamnatin kasar take yi domin kare hakkokin kananan kabilun kasar, da kira ga kasa da kasa su hada kai wajen yaki da kalaman hura wutar kyama.

Har wa yau, akwai kasashe da kungiyoyin da ba na gwamnati ba, wadanda suka soki Amurka da wasu kasashen Turai, saboda matsalolin da suke tattare da nuna kabilanci, da “tsoron addinin Musulunci”, da kuma yayata kalaman hura wutar kyama da wasu ‘yan siyasa suka yi.(Murtala Zhang)

Exit mobile version