Leadership News Hausa
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership News Hausa
No Result
View All Result

Kwararru Sun Yi Gargadi Kan Bada Biza A Cikin Kasa

by
2 years ago
in RIGAR 'YANCI
3 min read
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram
ADVERTISEMENT

Jami’an Diplomasiyya da kwararru a fannin tsaro sun bayyana ra’ayin su a kan abin da ya shafi tsaro da tattalin arziki dangane da sabon tsarin bayar da bizar nan da wannan gwamnatin ke da nufin aiwatarwa kamar yanda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya shelanta.

Tun a ranar 11 ga watan Disamba ne Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya shelanta cewa Nijeriya za ta fara bayar da biza ga dukkanin bakin nahiyar Afrika ne a bayan sun iso cikin kasar nan. Ya kuma bayyana wannan shirin ne a wajen taron Aswan kan samar da dawwamammen zaman lafiya da aka yi a kasar Misira.

Babban Kwanturolan hukumar shigi da fici ta kasa (NIS), Mohammed Babandede, cikin wata sanarwa ya yi bayanin yanda tsarin yake, yana mai cewa batun bayar da bizar a bayan bakin sun iso kasar nan ga dukkanin masu rike da Fasfunan kasashen Afrika, za a fara aiwatar da shi ne daga watan Janairu na shekarar 2020.

Labarai Masu Nasaba

Gwamnatin Jihar Zamfara Ta Tabbatar Da Kama  Wasu Sojoji Masu Hulda Da ‘Yan Ta’adda

Kansila Mai Mataimaka 18 Ya Sadaukar Da Albashinsa Na Farko

Amma a bayan mako guda da fadin hakan sai majalisar Dattawa ta yi watsi da wannan sabon shirin na bayar da takardar bizar bayan an shigo kasa, tana mai cewa lokacin yin hakan bai yi ba tukunna, musamman in an yi la’akari da yawaitar matsalolin tsaro a cikin kasar nan. a kan hakan har ta gayyaci Ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola, da babban Kwanturolan hukumar ta shigi da fici da su bayyana a gaban kwamitin ta na harkokin cikin gida, Shari’a da aokin Lauya domin su yi mata bayanin halascin wannan tsarin a tsarin mulki kafin a fara aiwatar da shirin.

In har aka kaddamar da wannan sabon tsarin a nan Nijeriya hakan yana nufin Nijeriya din ta bi sahun kasashen, Sierra Leone, Kenya, Rwanda da Habasha kenan, a matsayin kasashen da duk suke gudanar da wannan tsarin na bayar da biza ga bakin kasashen nahiyar Afrika a bayan sun shiga cikin kasahen na su.

Wani jami’in diplomasiyya kuma kwararre a kan harkar tsaro, ya shaida wa wakilinmu cewa, ya kamata a yi la’akari da yanda wannan sabon tsarin zai amfanar da tattalin arzikinmu, da kuma yanda abin zai iya shafan matsalolonmu na tsaro, musamman in an yi la’akari da yanda nahiyar ke cikin rigingimu iri daban-daban.

Duk masu ganin abin zai amfanar da tattalin arzikin mu ya zama tilas da su fara samar da hanyar toshe duk wata barazanar tsaro da shirin zai iya kawowa.

Shugaban kungiyar kwararru a kan hulda da kasashen ketare, Ambassada Gani Lawal, cewa ya yi, “In har za mu samar da tsarin bayar da biza a bayan baki sun shigo cikin kasar nan, hakan yana da kyau, sabili da cewa hakan zai kara saukaka wa sauran ‘yan Afrika hanyoyin yin kasuwanci da ‘yan’uwansu da ke nan Nijeriya.

Ambassada Lawal ya ce, duk da cewa tsarin ba ya rasa matsala da abin da ya shafi harkar tsaro, amma abu ne da za a rika aiwatar da shi sannu a hankali.

“Ba zai yiwu a rana guda komai ya kammala ba. Amma in mun fara aiwatar da shi a nan ne za mu fahimci duk wasu kura-kurai da ke a cikin sa muna toshe su, kamar abin da ya shafi sanya ido a kan masu shigowa.

Wani tsohon jami’in diplomasiyya, Ambassada Sani Saulawa Bala, shi ma cewa ya yi, “Bai kamata sabon tsarin ya kada wa wani hanta ba. Muna da isassun ma’aikatan da za su iya kulawa da shirin.”

Ya ce wannan tsarin na bayar da biza ga baki a bayan sun shigo kasarmu ai ba sabo ne ba, amma ‘yan Nijeriya suna ta bayyana fargabar su ne a kan abin da ya shafi matsalar tsaro domin a yanzun ne ake kaddamar da shi a nahiyar tamu.

Sai dai, Dakta Amaechi Nwokolo, kwararre a kan harkokin yawon shakatawa da ci gaba, ya bayyana damuwar sa ne a kan sabon tsarin bayar da bizar a bisa dalilai na tsaro, yana mai cewa ya kamata fa gwamnatin tarayya ta taka a sannu.

“Mun shirya wa kalubalen da ke cikin shirin?” in ji shi.

“Ana fama da rigingimu masu yawa a kasashen da suke a nahiyar Yammacin Afrika. Ya kamata mu dubi abin da za mu amfana da shi a kan tattallin arzikin mu.

“A yanzun kasashen Duniya ba su wadatuwa da tsaron kasashen su, suna ta faman neman hanyoyin da za su tsare kan iyakokin su. Amma mu muna son mu bar namu a bude wagaga.

“Kungiyoyin ‘yan ta’adda suna son kafa sassan su a ko’ina. Bai kamata mu karfafi ‘yan ta’addan su da suke cikin barci ba a nan Nijeriya, mu kara tabarbara lamarin tsaron kasar mu.

Ya ce, tabbas tsarin zai iya amfanar da tattalin arzikin mu, amma ya kara da cewa yawan masana’antun ma da muke da su ya yi karanci a halin yanzun da har z amu ce za mu bude kan iyakokin mu ga kowa ya shigo.

“Idan har gwamnati ta na shirin yin hakan ne a sabili da bunkasar tattalin arzikin wata kasa da kuma ita kanta nahiyar ta Afrika, abin da ma muke yi a halin yanzun bai wadata ba? wannan cin girman da mu ke yi ya isa haka nan,” in ji shi.

 

 

 

Like this:

Like Loading...
SendShareTweetShare
Previous Post

Yadda A Ka Gudanar Da Mauludin Mahaddatan Kur’ani Da Islamiyya Na Kano

Next Post

Kansilan Mazabar Tukur–tukur Ya Tallafa Wa Matasa 200 Kan Ilimin Kwamfuta

Labarai Masu Nasaba

Zamfara

Gwamnatin Jihar Zamfara Ta Tabbatar Da Kama  Wasu Sojoji Masu Hulda Da ‘Yan Ta’adda

by
1 year ago
0

...

Kansila Mai Mataimaka 18 Ya Sadaukar Da Albashinsa Na Farko

by
1 year ago
0

...

APC

Sanata Al-Makura Ya Cancanci Rike Kujerar Shugabancin APC, Inji Gwamna Sule

by
1 year ago
0

...

Kebbi

Bagudu Ya Bukaci ’Yan Nijeriya Su Zama Masu Kishin Kasa A Shafukan Sada Zumunta

by
1 year ago
0

...

Next Post

Kansilan Mazabar Tukur–tukur Ya Tallafa Wa Matasa 200 Kan Ilimin Kwamfuta

Domin bayar da talla ko neman ƙarin bayani a tuntuɓe mu a: +2348039216372

  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us | English Edition | Fashion Magazine | Business News

© 2022 Leadership Media Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2022 Leadership Media Group .

%d bloggers like this: