Connect with us

LABARAI

Kwararrun Barayi Ke Shugabancin Nijeriya –Shugaban JAMB

Published

on

Magatakardan hukumar shirya jarabawar shiga Jami’a, Is’hak Oloyede, ya ce, kwararrun barayi ne suka mamaye Nijeriya.

Shehin malamain na Jami’a ya fadi hakan ne ranar Asabar a Osun, lokacin da yake magana wajen bikin cikar Gwamnan Jihar ta Osun shekaru 61 da haihuwa.

Mista Oloyede, wanda ya yi jawabi kan, “Mahimmancin Nagartaccen Ilimi, Shi ne Tubalin Ginin Kasa Da Samun ‘Yanci,” ya ce, ilimi a kasarnan yana fuskantar barazana sabili da “kwararrun barayi ne ke jagorantar lamarin.”

Ya bayyana cewa, bambancin da ke tsakanin abin da magabatansa suka tara da kuma abin da shi kansa ya tara a hukumar, ya nu na a fili cewa an tafka cuwa-cuwa a hukumar ta JAMB.

“Barayi ne suka mamaye Nijeriya a sama, ina nufin kwararrun barayi. Bari na bayar da misali da hukumarmu ta JAMB, tun da kafa hukumar ta JAMB sama da shekaru Arba’in, jimillan kudin da hukumar ta tara har kafin zuwa na cikinta shi ne, Naira milyan 52.

“Bayan mun kammala jarabawanmu na shekarar 2017, mun tara Naira bilyan 9, inda na mayar wa da gwamnatin tarayya Naira milyan 7.8. Wakilan Majalisar kasa sun yi mamakin faruwar hakan, a wannan shekarar ma na tara sama da Naira bilyan 9,” in ji shi.

Sai magatakardan na JAMB, ya yi dirar mikiya a kan halayen banza kamar na kungiyoyin asiri da karuwanci da ke kara yawaita a manyan makarantunmu.

“Ba sai ka yi amfani da Bam ne za ka iya tarwatsa kasa ba, ka lalata lamarin ilimin su kadai, ka bari dalibai su yi ta magudi a wajen jarabawa. Ilimi ne kadai zai iya gyara halayyan al’umma.

“Tilas ne a sami nagartaccen ilimi in ana son a fitar da al’umma daga kangin talauci da wahala. A jimlace, tilas ne a sami nagartaccen ilimi kafin ya zama mai amfani.”

Ya bukaci ‘yan Nijeriya da su tabbatar da cewa, dalibai su na yin aiki da abin da suka koya, “Domin ma’anar karatu ba takardar shaida ne kadai ba, har ma da yin aiki da shi.”

 
Advertisement

labarai