Daga Umar Faruk,
Hukumar Kwastam ta Nijeriya (NCS), reshen jihar Kebbi, ta cafke haramtattun kayayyaki na Naira miliyan 320 tsakanin watan Janairu zuwa Disamba na shekarar 2020.
Da yake zantawa da manema labarai ranar Laraba a Birnin Kebbi, Kwanturolan yankin na Kwastam, Hafiz Kalla, ya ce ayyukan rundunar a shekarar 2020 sun fi mayar da hankali ne kan dakile fasa kwabri, yana mai jaddada cewa an rufe iyakokin tudu a cikin shekarar da ta gabata.
“Don haka, mun kasance a shirye don tabbatar da cewa ba a ba wa masu yi wa tattalin arzikin zagon kasa sarari ba. A karshen wannan, kokarin da muke da shi cikin nasara ya sami nasarar kama kayan fasa kwabri guda 227 a shekarar da ta gabata.
Kalla ya bayyana cewa kayayyakin da rundunar ta kama sun hada da buhuna 333 masu nauyin kilogiram 1 kowanne na tabar wiwi, buhu biyu na maganin Diazepam 5mg da buhunan power snuff guda 121.
“Sauran su ne buhu 3,999 mai nauyin kilogiram 50 na takin zamani na kasashen waje sai kuma Buhu 2,021 na shinkafa mai nauyin kilogiram 50 ‘yar kasar waje, buhu 19 na shinkafa mai nauyin kilogiram 100 ‘yar kasar waje, haka kuma da katun 20 mai nauyin kilogiram 25 na shinkafar waje.
“Har ila yau, muna da dila 607 na kayan gwanjo, buhu 68 na sababbin takalmin daga kasar waje, sai kuma zanen atamfa bandir 23,450, buhuna 395 na lita 25 na dabino da aka shigo da su da kuma kayan lambu.
“Sauran sun hada da buhunan sukari 91 na kasar waje mai nauyin kilogiram 50kg, da manyan motoci hudu da sauransu. Mun kuma kwace wukake da jarkoki 260 da motoci 70 da aka yi amfani da su wurin dauko kayan; da sauran abubuwa daban-daban.” In ji Kwanturolan.
A cewar sa, kudin harajin da ya kamata a biya na wadannan abubuwan da aka ambata sun kai Naira 320,701,566.
Kalla ya kara da cewa, a daidai wannan lokacin, an kama tare da gwanjon lita 126,005 na manfetur da dizal tare da wasu abubuwa masu lalacewa.
“Kayayyakin da aka yi gwanjon sun samar da jimillar Naira 35, 329,000, kuma an sake shigar da irin wannan a cikin Asusun Tarayya kamar yadda doka ta tanada,” in ji shi.
“Nasarorin da aka samu a sama ya kasance ne sakamakon aiki tukuru, kwazo da kuma yin taka tsan-tsan da jami’anmu da mazajenmu suka nuna a wannan fagen. Kuma tabbas, tare da taimako da goyan bayan wasu sassan a cikin sabis da hukumomin tsaro masu dacewa ta hanyar hadin kai da musayar bayanan sirri,” in ji shi.
Kwanturola Hafiz Kalla, ya sake nanata irin jajircewa da kuma sadaukarwa da jami’an rundunar suka yi domin dakile matsalar fasa-kwauri a Jihar Kebbi da kasa bakidaya.
Ya yi kira ga al’ummar jihar da su ci gaba da ba da hadin kai da taimakawa da bayanai masu amfani domin kare kasar nan daga shigo da kayayyaki masu illa ga lafiyar ‘yan kasa da tattalin arzikin kasa Nijeriya.