Abubakar Abba" />

Kwastam Ta Gargadi Masu Safarar Kayayyaki Daga Kasashen Waje

Hukumar hana fasa kwauri ta ja kunnen masu sarrafa kayayyaki da fitar dasu zuwa kasashen waje dake kasar nan dasu guji fitar da kayan da gwamnati ta haramta.

Shugaban hukumar na shiyya Yamma Aminu Dahiru ne  ya yi gargadin a lokacin kudanar da taron lacca karo na farko na shekara da shiyyar ta gudanar a jihar Legas, inda ya ce hukumar a shirye take ta kwace irin wadannan kayan da kuma hukunta duk wanda ta kama. Dahiru ya ci gaba da cewa, dukkan kayan da ake sarrafawa a cikin gida ana fitar da su ne kai tsaye, ha kan kuma ba zai  zamo wata dama ba ga marasa kishin kasar  su dinga fitar da kayan da aka haramta ba.

A cewar sa, “Jami’ai na suna nan suna sanya ido a kan irin wadannan kayan da ake fitar dasu daga cikin kasar nan, inda ya buga misali da Timba ko wacce iri ce.

Shi ma a nasa jawabin, Babban Sakataren cibiyar  masu safarar kayayyaki zuwa kasar waje Hassan Bello, ya bayyana cewa, cibiyar tana kan kammala shirye-shirye don yin hadala da Ma’aikatar Noma don bunkasa fitar da amfanin goma zuwa kasashen duniya.

Bello kasidar sa mai taken ,”Gudunmawar da fitar da kayayyaki zuwa kasar waje suke takawa don inganta kayan da ake fitara a Nijeriya” ya ce, cibiyar ta tattauna da Babban Bankin kasa  CBN da bankin fitar da kaya da sauran su akn yadda za’a taimakawa yan Nijeriya masu fitar da kaya zuwa kasashen duniya da kuma manoma a kan yadda zasu dinga futar da kayayyakinsu zuwa kasar waje.

Bello, wanda  Daraktan Ayyuka na Musamman da kuma yada kabaran cibiyar Ignatius Nweke, ya wakilce yaci gaba da cewa, cibiyar tana kan tattaunawa da hukumar fitar da kayayyaki zuwa kasar waje din taimawa cibiyar mu a kan fitar da kayayyaki zuwa kasar waje.

Acewar sa, a yanzu haka “ hukumar munyi hadaka da ita din yin aiki kafada da kafada a kan yadda za ta balu kwarun gwaiwa wajen fitar da kayayyaki zuwa kasashen duniya.”

Ya bayyana cewar, cibiyar ta kafa cibiyoyin samar da bayanai a sasssa da ban-da-ban na kasar nan don samun bayanai a kan yadda za’a tunkari yadda za’a dunga fitar da kaya kasashen waje.

Bello ya sanar da cewar,“muna kuma yin dubi a kan yadda zamuyi hadaka da sashen gwamnati da kula shirye-shiryenta data keyi a kan yaki da cin hanci da rashawa da kuma shirye-shiryenta na noma har ila yau, muna yin dukkan wannan ne don bin ka’idojin da aka gundaya na futar da kayayyaki zuwa kasar waje.”

Babban Sakataren ya bayyana cewar,” idan mukayi dubi a kan bayanai za’aga cewar a shekarar 2917 kamar yadda hukumar kididdiga ta kasa ta sanar, munada jimlar  kayayyakin da aka fitar da suka kai na naira biliyan 3.9 a zangon shekara na hudu  a shekarar data gabata wanda ha kan ya karu da kashi talatin da biyar bisa dari sama da adadin da aka samu a zangon shekara na uku.

Acewar sa, “ muna yin dubi ne a kan kasshen da muke yin kasuwanci  dasu, inda a farkon shekarar 2018, munada kasar Indiya, Netherland, Spaniya, Amurka, Faransa, Afirka ta Kudu , Birtaniya da kuma Indonesiya kuma a kwai adadi da dama kuma in har bamu bayar da goyon baya ba  wajen fitar da kaya daga Nijeriya ba, tattalin arzikin kasar bazai yi daidai ba.”

Exit mobile version