Hukumar Kwastam ta Nijeriya reshen jihar Kebbi, ta kama jimillar lita 35,725 na man fetur da sauran haramtattun kayayyaki da darajarsu ta kai sama da Naira miliyan 109.5 a wani sabon farmakin da ta kaddamar kan fasa kwabri a kan iyakokin jihar.
Kwanturolan hukumar na jihar, Mahmoud Ibrahim ne ya bayyana haka a lokacin da yake ganawa da manema labarai a hedikwatar hukumar da ke Birnin Kebbi ranar Laraba.
Ibrahim ya ce an kama mutanen ne ta hanyar hadin gwiwa da rundunar ‘Operation Whirlwind’, runduna ta musamman ta hukumar.