Abubakar Abba" />

Kwastam Ta Kwace Kayyakin Naira Biliyan 2.713 – Ali

Hukumar Hana Fasa Kwauri ta kasa ta sanar da cewa, ta kwace Sundukan shinkafa, da nagungunan tiramadol da kuma waau magunguna marasa rijista da kudisu su ka kai naira 2,713,865,051.

A ranar Talata ne Kwanturola Janar na Hukumar Kanal Hameed Ali mai ritaya ya  sanar da hakan a lokacin da ya gabatar da kayyakin da hukumar ta kwace a jihar Legas, inda ya ci gaba da cewa, kwace kayayyakin yana daya daga cikin nasararorin rufe bakin iyakokin Nijeriya da gwamnatin tarayya ta bayar da umarnin ayi na wucin gadi.

Ya kara da cewa, kwacen kayan, wadda Rundunar Tsibirin TinCan ta TinCan Island  dake cikin jihar Legas ta jagoranta, ya hada da Sundukan buhunhunan shinkafa 33, Sundukin  shinkafa daya wadda aka rufe ta da kayan gyara da kuma kwantenoni 11 na magunguna marasa rijista.

A cewar Ali, kwace kayan ya kuma hada da Sundukai biyu na tsofaffin tayoyi da Sunduki daya ta tsofaffin tufafi da Sundukai hudu  na man girki, inda ya kuma sanar da cewa, kuma  dukkan kwacen yana cikin tanadin dokar gudanar da aikin na  hukumar ta kwastam.

Ya yaba wa jami’an TinCan Island a bisa  nanijin kokarin da suukayi na karbe kudade shiga da su ka kai naira 286,742,551,443 tun daga watan Janairu, inda ya yi nuni da cewa,abu ne da kowa ya sani cewa hukumar ta kwastam, tana jagorantar sauran hukumomin tsaro wajen aikin hadin gwiwa da aka sa wa suna ‘Ed Swift Response’ da ofishin nai baiwa  Shugaban kasa  shawara a kan harkokin Tmtsaro ke kula da shi.

Ya kuma bayyana cewa, hukumar kula da shige da fice, da haɗmdin guiwar Rundunar Sojin kasar nan da Rundunar  yan Smsanda ta kasa da jami’an hukumomin Tmtsaro na sirri suna nan suna tabbatar da rufe bakin iyakokin na Nijeriya na wucin gadi.

Aki ya ce, tunda aka fara aikin, kwace kayayyaki masu yawan gaske, a duk fadin yankuna daban-daban da muke aiki kuma abu ne da aka sani cewa rufe bodar da aka yi na wucin gadi ya taimaka wajen dawo da jiragenmu na daukar kaya zuwa tekuna, kuma wannan ya bada damar kwace  kaya, masu yawan gaske wadanda ba don haka ba da tuni an shigo da su ta bakin iyakokin ba bisa ka’ida ba.

Ya sanar da cewa, buhunan shinkafar da aka kwace ko dai sun lalace ko kuma sun kusa lalacewa, inda ya kara da cewa, hukumar ta fadakar ta kuma jawo hankalin al’umma zuwa ga gaskiyar cewa da yawa daga cikin shinkafar da aka shigo da ita lalatacciya ce.

Ali ya ce, tun a baya, hukumar ta fito da hadarin amfani da kwayar tiramadol ta kuma kwace tare da fara lalata tiramadol da kuɗimdinsa  ya kai naira biliyan 14 kwanan nan, inda kuma ya nuna takaicinsa cewa wadanda ke shigo da kaya masu hadari ba sa nufin mu da alheri.

Ya bayyana cewa, akwai abinda zai faru da a ce sun yi nasarar shigo da lalatacciyar shinkafar, sake mata buhu, su kuma canza mata kwanan watan lalacewa don ‘yan Nijeriya su ci kuma za’a  iya tunanin mummunan tasirin da cin wannan shinkafa zai iya yi, kafin a iya ji a jiki.

Ya yi nuni da cewa, don a guje wa shakka, bari in nanata koƙarin hukumar da sauran hukumomi ‘yan uwanta na tsare bakin iyakokinmu na kasa daga wadannan kaya masu hadari, inda ya kara da cewa, wannan gargadi ne ga dukkan mashigar ruwa da mafitar ruwa cikin kasar nan.

Ya kara da cewa,  tuni ya bada umarni a yi cikakken bincike don gurfanar da dukkan wadanda ke da dangantaka da shigo da kayayyakin gaban shari’a, inda kuma ya zaiyyana cewa, magungunan da aka kama sun hada da  kwayar magani ta chlorokuine mai nauyin kilogiram 20, Hyergra 120, Artesam, allurar Bitamin B compled, Comefwn Forte da sauransu.

Exit mobile version