Connect with us

TATTALIN ARZIKI

Kwastam Ta Samar Da Harajin Biliyan N573 Cikin Wata Biyar

Published

on

Hukumar Kwastam ta Nijeriya ta samu nasarar samar da haraji wanda ya kai naira 573,190,265,605.41 tsakanin watan Junairu zuwa watan Mayun shekarar 2020. Shugaban sashin kudade na hukumar, Sadik Ibrahim Ismailia, shi ya bayyana hakan lokacin da wakilan hukumar Kwastan wanda mataimakin shugaban hukumar Kwastam, DCG Sanusi Abubakar Umar, yake jagoranta suka gurfana a gaban kwamitin hukumar Kwastan na majalisar dattawa a garin Abuja.

Shugaban kwamitin hukumar Kwastan a majalisar dattawa, Sanata Francis Ailimikhena wanda yake wakiltar Jihar Edo ta Arewa, ya bayyana cewa, wannan tattaunawa yana daya daga cikin wani bangare na bincikan ayyukan kasafin kudi na shekarar 2020 na hukumar, a dai cikin wannan kudade akwai na kayayyakin da aka kwace da kuma kayayyakin da aka yi gwanjansu.

Ismailia ya ce, “a tsakanin watan Junairu da watan Mayun shekarar 2020, an samu ayyukan kasafin kudi wanda ya kai na naira 37, 865, 867, 750 wanda ya kai kashi 15.90 na kasafin kudin hukumar.

“Hukumar ta yi tsammanin samar da kudaden haraji na naira tiriliyan 1.6, amma sakamakon cutar Korona ta sa an samu naira biliyan 957. Daga watan Junairu zuwa watan Mayu hukumar ta tattara haraji wanda ya kai na naira 573, 190, 265, 605.41.”
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: