Connect with us

LABARAI

Kwastan Ta Cafke ’Yan Fasa Kauri A Jihar Katsina

Published

on

wato kwastom ta bayyana cewa ta baza komarta domin tabbatar da ganin ba’a shigo ko fitar da kayayyakin da aka haramta shigowa dasu a kasar nan.
Jami’in hulda da jama’a na hukumar, mataimakin sufurutandan na kwastom Theoplus Duniya ya bayyana haka yayin da yake zantawa da manema labarai a hedkwatar hukumar dake Katsina.
Ya ce hukumar na cigaba da kokari domin tabbatar da ganin an dakile shigowa da kayayyakin da aka haramta shigowa dasu da kuma makamai domin ganin an damke da kuma hukunta masu aikata wadannan ayyuka.
Mai magana da yawun hukumar ya ce jihar Katsina na daya daga cikin jihohin dake kan iyakar kasa, yana mai cewa jami’an hukumar a koda yaushe na cigaba da sintiri domin tabbatar da ganin ba’a shigo da makamai ba’a kasar nan ganin cewa manyan zabukan shekarar 2019 na kara kusantowa.
Akan sha’anin shigowa da shinkafa, Mr. Theoplus Duniya ya ce gwamnatin tarayya na yin dukkanin mai yiyuwa domin tabbatar da ganin an rage shigowa da shinkafa.
Haka kuma jami’in hulda da jama’a na hukumar ya yabama sarakunan Katsina da Daura bisa goyon bayan da suke ba hukumar wajen aiwatar da ayyukansu na kasa.
Don haka ya yi kira ga daukacin al’umma da sauran hukumomin tsaro dake aiki a jihar nan dasu ba hukumar dukkanin goyon bayan da ya kamata wanda zai taimaka masu wajen shigowa da haramtattun kayayyaki a jihar nan.
Hukumar ta kastam reshen jihar Katsina tana nan tana ta artabu da yan fasa kwauri ba dare ba rana wanda har ta kasance ba makawa saida suka bi gida gida suna bankado kayan fasa kwauri da aka boye wanda har takai ga dukanin wani shugaban yan fasa kwabrin wanda wata majiya ke cewa an tafi dashi zuwa Abuja domin karasa wasu bincike. Tuni dai jihar Katsina da su yan fasa kwabrin ake ta takon saka hart a kai ana uwarka ubanka da sauran fadace-fadace wanda tilas sai gwamnati ta shiga Tsakani
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: