Kwastan Ta Kwace Jarka 2,200 Na Haramtaccen Fetur

Hukumar Kwastan ta kasa(NCS) dake kan iyakar Same ta sanar da cewar ta kwace jarkokin haramtaccen man fetur 2,200 da aka yo fasakwarun su wadanda aka kiyasta kudin su ya kai samada naira miliyan goma a tsaknin watan daya na Disambar shekarar 2017 ya  zuwa yau.

Kwantirolan shiyyar Mohammed Aliyu ya sanar da hakan jiya Litinin a sanar da  kakakin rundunar na shiyyar Mista Taupyen Selchang a ya fitar.

Kwantirolan yace, mafi yawanci kayan da aka kwace, an yi sune a yankin Pashi-Yekeme dake cikin  Owode da kuma creeks.

An ruwaito cewar, yawan jimlar mai da aka fi sami (PMS) da hukumar ta kwace, ya kai yawan litoci 55,000 idan akan buga akan 2,200 na kitoci 25.

Mohammed ya ci gaba da cewa, rundunar, a shirye take don ganin ta magance yin fasa kaurin na mai da dangogin sa, kamar yadda masu fasa kaurin suke shigo da man ta yin amfani da jarkoki ta hanyar iyakar.

Kwantirolan ya sanar da cewar, ba wai sun haramta yin amfani da manyan motoci bane wajen yin dakon man zuwa cikin alumomi bane, ta gefen iyakar, in har an yo jigilar man ta halastaciyyar hanya sabanin yadda wasu mutane suke yamadidi ba.

Mohammed ya kara da cewa, yin fasa kwarin man a cikin jarkoki, ya ragu sakamakon kokarin dakile hakan da jami’ain hukumar suke yi a kodayaushe.

A cewar sa, “ wannan shine goyon bayan da muke bayarwa don kawowa ‘yan Nijeriya saukki sakamkon halin kuncin da wasu suka jefa su na karancin man.”

A karshe Kwantirolan yace rundunar, zataci gaba da yin amfani da karfin ikonta wajen samarwa da gwamnati kudin shiga da kuma dakile fasa kauri musaman a iyakokin kasar nan.

 

Exit mobile version