Kwanturola-Janar na Kwastam (CGC), karkashin ‘Strike Force Team, Zone B’, sun kwace kayayyakin da yawansu ya haura Naira miliyan 67 da aka shigo da su kasar nan ta kan iyakokin Jihar Katsina a cikin kwanaki 40 da suka gabata.
Shugaban rundunar, Mataimakin Kwanturola, Olorukoba Oseini-Aliyu, ne ya bayyana hakan a ranar Talata a Katsina, yayin da yake zantawa da manema labarai game da kayayyakin da aka kama, yana mai cewa an kame kayayyakin ne tsakanin 11 ga Oktoba zuwa 20 ga Nuwamba, 2020.
Daga cikin kayayyakin da aka kama sun hada da buhunan shinkafa 396 na kasar waje, dilar gwanjo 319, motoci biyu, sannan akwai wasu motocin guda bakwai ana tsare da su, katan 57 na madara da alawa da kuma katan 17 na spaghetti na kasar waje.
“Ganin sabuwar shekara na karatowa, wasu masu fasa-kwauri na son yin amfani da wannan damar wajen shigo da haramtattun abubuwa cikin kasar nan,” in ji shi.
Ya shawarci masu fasa-kwauri da su sauya tunaninsu zuwa mafi kyawu kuma su koma kasuwancin da kasa ta amince dashi, sannna ya kara shawartar ‘yan Nijeriya da su daina mu’amala da kayayyakin da ake shigo da su ta barauniyar hanya don kiyaye lafiyar su da inganta tattalin arzikin kasa.