Kwastom Sun Cika Hannu Da Tankar Mai Dauke Da Shinkafa Buhu 210 A Katsina

Daga El-Zaharadeen Umar,

Hukumar hana fasa kwabri ta kasa wato kwastan ta yi nasarar cafke wata motar daukar Mai da aka yi amfani da ita wajan yin fasa kwabrin shinkafa ‘yan kasar waje da gwamnatin Najeriya ta haramnta shigowa da ita daga wasu kasashe.

Shugaban hukumar Kwastan a jihar Katsina, Adewale Musa Arewa ya bayyana haka ga manema labarai a lokacin da yake nuna yadda masu fasa kwabri suke amfani da tankar daukar mai domin shammatar jami’an su kafin daga baya su damke wannan mota.

Kamar yadda ya bayyana ita dai wannan mota an kama ta ne a garin Dutsinma bayan da jami’ansu suka sami labarin cewa an zubo shinkafa ‘yan kasar wajen har buhu 210 a cikinta, a maimakon mai da aka san ana dauka a cikin motar.

Motar wanda aka ga an lika mata tambarin kamfanin mai na A.A Rano amma na boge, an samu nasarar damke mutanen da ke cikinta tare da kama wani mutun daya da ya zo shalkwatar kwastan din ya bayyana kansa a matsayin mamalakin wannan mota.

Ya ce zuwa yanzu suna cigaba da gudanar da bincike akan wadanda suka kama game da wannan mota, kafin daga bisani su dauki matakin da shari’a ta zayyana akan masu wannan danyen aiki na fasa kwauri

Ita dai wannan mota kamar yadda shugaban hukumar kwastan ya nunawa manema labarai shi ne, an yi mata wani irin tsari a cikinta, ramin dauka mai daya ne kawai ya rage sauran wurin ararakeshi an maida shi wani abu na musamman domin daukar shinkafa.

Kazalika sun kara kama wasu motocin da aka yi kokarin shigawa da su ba bisa ka’ida ba inda ya kara da cewa sun kama wata mota kirar BNW 2014 wanda kuma ya kamata a biya harajin miliyan uku akanta sai kuma wata motar kirar Toyata Hilud 2020 wanda ita ya kamata a biya miliyan shida a matsayin kudin harajinta.

Haka kuma ya kara da cewa sun samu nasarar damke wata mota kirar Toyota Land Cruiser wanda ya kamata a biya kudin haraji naira miliyan 17, a cewarsa hatta motar da ta dauko shinkafa sun yi mata kudi naira miliyan 13.

Adewale Aremu yana mai gargadin masu fasa kwabri a jihar Katsina da su san cewa shida yaransa basa barci saboda haka duk wata sabuwar dibarar da suke amfani da ita ba zata yi aiki ba a wannan lokaci.

Shugaban hukumar ya ce suna hada hannu da kungiyar masu saida mai ta kasa reshen jihar Katsina domin ganin an kwacewa faruwa irin wannan lamari, sai dai ya ce a mafiywan lokuta abinda ‘yan kungiyar masu saida man ke gaya masu daban abinda suke gani daban.

“Saboda haka yanzu ba zamu tsaya sauraransu ba, zamu cigaba da yin aikin mu kamar yadda aka saba, sai dai fa har gobe ba sani ba sabo akan duk wanda ya karya doka, zaman lafiya shine a bi doka a zauna lafiya,” inji shi.

Exit mobile version