Connect with us

MANYAN LABARAI

Kwastom Ta Kori Jami’in Da Buhari Ya Karrama Saboda Kin Karbar Rashawa

Published

on

Hukumar Kwastom ta Nijeriya ta kori jami’inta da ya yi fice wurin yaki da cin hanci da rashawa, Bashir Abubakar, ta kuma sallami wani jami’inta mai mukamin Mataimakin Shugaba mai suna Aminu Dahiru. Sanarwar da Kakakin hukumar ya fitar ta ce, an kore su daga aiki ne bayan samun su da sakacin aiki.

Hukumar Hana Fasakwaurin ta yi wannan hukunci dab da karshen mako, inda ta sanar da korar jami’inta mai mukamin mataimakin shugaba (ACG) Aminu Dahiru da kuma tilasta wa wani jami’in, ACG Bashir Abubakar, yin murabus, a cewar sanarwar.

ACG Bashir Abubakar dai shi ne jami’in da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya karrama da lambar girmamawa a shekarar 2019, saboda kin karbar toshiyar baki ta Dalar Amurka 412,000 kamar yadda majiyarmu ta ruwaito.

An kori jami’an biyu ne bayan samun su da laifin sakaci a watan da ya gabata kamar yadda binciken da kwamitin ladabtarwa da a ka kafa ya bayyana. An tuhumi ACG Aminu Dahiru da hannu a badakalar fasakwaurin manyan motoci guda 295 dauke da man fetur a watan Disambar 2019 lokacin ya na aiki da Rundunar Kare Kan Iyakokin Kan Tudu na Kasa.

Shi kuma ACG Bashir Abubakar a na zargin sa da bayar da umarnin yin samame a rumbun ajiyar shinkafa ’yar gida a kokarinsa na gano shinkafar waje a rumbunan ajiyar wani fitaccen mutum a garin Daura da ke Jihar Katsina.

A Nuwambar 2019, Shugaba Buhari da Shugaban Hukumar Kwastom, Hamid Ali, su ka karrama Bashir Abubakar da lambar yabo bisa gaskiyarsa da jajircewa a wurin aiki. Bashir Abubakar ya kuma samu yabo daga hukumar a shekarar 2018 bayan da ya ki karbar toshiyar baki ta Dalar Amurka 412,000 daga hannun wasu da su ka shigo da haramtattun kwayoyin Turamadol lokacin ya na kula da rundunar a shiyyar Apapa a Legas, lamarin da ya sa ya yi fice.

Har wa yau, Sanarwar ta ce rundunar ta yi wa wasu jami’anta 2,634 karin girma tare da tabbatar da nadin masu taimakawa shugaban rundunar guda biyar.
Advertisement

labarai