Muhammad Maitela" />

Kwaya Ce Ta Kashe Budurwar Da Aka Samu A Masaukin Bakin Yobe – ’Yan Sanda

A sanarwar da rundunar ‘yan sandan Nijeriya da ke jihar Yobe, ta bayyana cewa binciken da ta gudanar ya nuna shan miyagun kwayoyi ne ya yi sanadin mutuwar budurwa nan yar shekaru 18, wadda aka tsinci gawarta a masaukin bakin gwamnatin jihar da ke birnin Damaturu a mako da ya gabata.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar a jihar Yobe, ASP Dungus Abdul-Kareem shi ne ya bayyana hakan a ranar Talata, wanda ya kara da cewa, binciken nasu ya tabbatar da cewa matashiyar- Bilkisu Ali, ta mutu ne sakamakon kwayoyin da ta sha fiye da kima.

Bugu da kari kuma, tun a ranar 7 ga Janairun 2021 rundunar ‘yan sandan ta kama Al-bash Yahaya Ibrahim tare da wasu mutum uki wadanda take zargi da laifin kisan budurwar.

Al’amarin da ya jawo ci gaba da tsare wadanda ake zargin tare da ajiye gawar matashiyar asibiti har lokacin da aka kammala binciken abinda ya yi sanadin mutuwarta.

ASP Dungus ya kara da cewa, rundunar ‘yan sandan za ta mika wadannan mutum hudu da ake zargin a gaban kotu domin amsa tuhume-tuhumen da ake musu wadanda su ka hada da zargin hada baki wajen aikata laifin kashe budurwar da aikata zina.

A hannu guda kuma, rundunar ‘yan sandan jihar Yobe ta gargadi jama’a su guji yada jita-jita maras tushe wadanda za su jawo rudani ga yan uwa da makusantan marigayiyar kana barazana ga tsaro a jihar.

 

Exit mobile version