Connect with us

DAGA BIRNIN SIN

Kwayar Cutar COVID-19 Da Take Yaduwa A Kasashen Faransa Da Canada Ba Ta Fito Daga Kasar Sin Ba

Published

on

Wani nazarin kwayoyin halittar gado da wasu masanan kasar Faransa suka gudanar ya nuna cewa, cutar COVID-19 da ta bullo a kasar ta Faransa, wata kwayar cuta ce da ke yaduwa a cikin kasar da ba a san asalinta ba ta haddasa, ba daga kasar Sin ko Italiya ba, kamar yadda wasu ke fada a baya.

Masana daga cibiyar Pasteur dake birnin Paris, cibiyar da ta shahara wajen bincike kan cututtuka masu yaduwa ta fitar da sakamakon nazarin, mai taken, “Gabatarwa da farkon yaduwar SARS-CoV-2 a Faransa” aka kuma wallafa shi a shafin Biorvix.org a ranar 24 ga watan Afrilun wannan shekara.
Masanan sun jera kwayoyin halittu 97 daga samfura da suka tattara daga jikin wadanda suka kamu da cutar a kasar Faransa daga ranar 24 ga watan Janairu zuwa 24 ga watan Maris, inda suka gano cewa, yanayin barkewar cutar a kasar, yana da nasaba da rukunin kwayoyin halittar ko rukunin clade G wanda ba shi da nasaba da kasar Sin ko Italiya. (Ibrahim)
Kafafen yada labarai na kasar Canada, sun bayyana cewa, bayanai daga manyan lardunan kasar sun nuna cewa, kwayar cutar da ta harbi mutane na farko-farko a kasar ta fito ne daga Amurka maimakon kasar Sin.
Jaridar National Post ta ba da rahoto a ranar 30 ga watan Afrilu cewa, bayanai daga manyan lardunan kasar da suka hada da Ontario da Quebec da British Columbia da Alberta, sun nuna cewa, masu yawon bude ido daga Amurka dake dauke da kwayar cutar ce suka shigo da ita kasar ta Canada. (Ibrahim)
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: