Kyakkyawan Jagoranci: Mafarauta Sun Koma APC A Kumbotso

Mafarauta

Daga Abdullahi Muhammad Sheka,

Sakamakon  kyakkyawan jagoranci da kakarin kawo kowa cikin ayyukan alkhairin da  shugaban karamar Hukumar Kumbotso Alhaji Hassan Garba Farawa yake yi wa  al’umma yasa kungiyar  mafarauta karkashin jagorancin Sarki Lukman Panshekara da Sarkin dawa suka dawo tafiyar APC karkashin Shugabancin Hassan Garban Kauye Farawa.

 

An karcesu  a sakateriyar mulki ta   karamar  Hukumar  Kumbotso  inda suka  sami  rakiyar   Mai taimakawa Gwamna Kan ayyuka na musamman (S.A ) Alhaji Murtala  Gwarmai.

 

Da yake gabatar da jawabinsa alokacin bikin karbar wadannan Mafarauta, Shugaban Karamar Hukumar Kumbotso Alhaji Hassan Garban Kauye Farawa  ya  godiwa  ga  Allah  bisa  wannan  nasara da ya samu  inda ya ja hankalinsu  da su  dauki  amana  kamar  yadda  aka daukesu.A karshe  ya basu kudi  naira  dubu  dari  biyar  domin  su jika  makoshinsu.

 

Jagoran mafarautar ya bayyana godiyarsu tare da yin alkawarin aiki tare domin ciyar da yanki gaba.  Haka Kuma sun dauki  alkawarin  yin biyayya  a wannan  tafiya. Kamar yadda Mataimaki na musamman Kan harkar sadarwar zamani ga Shugaban Karamar ta Kumbotso Salmanu  Garba  Barista ya Shaidawa LEADERSHIP A Yau.

Exit mobile version