Connect with us

RAHOTANNI

Kyakkyawan Zumuncin Da Ke Tsakanin Shugabanni Da Al’ummomin Sin Da Rashai

Published

on

A yayin taron dandalin tattaunawar batun tattalin arziki na yankin gabashin

duniya karo na 4 da aka kammala kwanan baya, shugaban kasar Sin Xi Jinping

da takwaransa na kasar Rasha Vladimir Putin sun gana da juna, ganawar da ta

kasance na uku cikin watanni hudu da suka gataba. A hakika, yadda

shugabannin kasashen biyu suka sha ganawa da juna ya zama wata muhimmiyar

alama ta huldar da ke tsakanin kasashen biyu. A hakika, cikin shekaru sama

da biyar da suka gabata, shugaba Xi Jinping da shugaba Vladimir Putin sun

gana da juna har sau sama da 20, lamarin da ya nuna kyakyyawar dangantaka

dake tsakanin kasashen biyu, da kuma yadda kasashen biyu suka sanya

muhimmanci a kan huldarsu ta fannin harkokin diflomasiyya.

Jagorancin shugabannin kasashen biyu sun kara karfafa huldar da ke tsakanin

kasashensu. Yadda shugabannin kasashen biyu suka sha ganawa da juna, tare

da bullo da tsare-tsare ga ci gaban huldar abokantaka a tsakanin

kasashensu, sun taimaka ga ci gaban huldar kasashen biyu. Baya ga haka,

yadda shugabannin kasashen biyu suka yi ta kokarin shirya manyan bukukuwa

da shirye-shirye a tsakaninsu ma ya taimaka ga ci gaban hadin gwiwarsu.

A kokarin da shugabannin suka yi, huldar da ke tsakanin kasashen biyu sun

shiga wani sabon yanayi na samun inganci da saurin ci gaba. Baya ga

kyautatuwar tsarin ciniki a tsakaninsu, kasashen biyu sun kuma ingiza jerin

shirye-shiryen da suka shafi zuba jari da makamashi da sufuri da manyan

ayyuka da sauransu, har ma an gano sabbin fannonin da suka fara hadin

gwiwa, ciki har da kimiyya da ayyukan gona da ciniki ta yanar gizo da

sauransu.

Cudanyar jama’a na da muhimmanci wajen yin mu’ammala tsakanin kasashe.

Shugabannin kasashen biyu sun fahimci muhimmiyar rawar da mu’ammala a

tsakanin jama’arsu za ta taka sosai, idan har ana son kafa tushe sosai na

ra’ayin jama’a, za a iya kafa babban gini na sada zumunta a tsakanin

kasashen Sin da Rasha daga zuriya zuwa zuriya. A watan Yulin bara, shugaba

Xi da shugaba Putin sun sa hannu kan wata hadaddiyar sanarwa game da

zurfafa dangantakar abokantaka ta hadin kai bisa manyan tsare-tsare a

dukkan fannoni a tsakanin Jamhuriyar Jama’ar kasar Sin da Tarrayar kasar

Rasha a birnin Mosccow, inda suka jaddada cewa, yin mu’ammala tsakanin

jama’a da yin cudanyar al’adu muhimmin sashe ne na sada zumunta a tsakanin

kasashen biyu daga zuriya zuwa zuriya.

A yayin taron dandalin tattaunawar harkokin tattalin arziki na gabashin

duniya karo na hudu da aka shirya a ranar 12 ga wata, shugaba Xi Jinping ya

bayar da wani labari game da cudanyar jama’ar kasashen biyu: cibiyar

All-Russian Children’s Center “Ocean” dake Vladivostok ta taba karbar yara

sama da 900 da suka bukata daga bala’in girgizar kasa da ta faru a yankin

Wenchuan na lardin Sichuan na kasar Sin, wadannan yara sun samu kulawa

sosai a cibiyar, har sun sada zumunta sosai da Rasha. Wani daga cikinsu mai

suna Xi Junfei ya bayyana fatansa na yin karatu a Rasha idan ya girma.

Yanzu kuma ya cimma burinsa, yana karatu a jami’ar gabas mai nisa ta Rasha

mai suna Far Eastern Federal.

Haka kuma, bisa jagorancin shugabannin biyu, zumuncin dake tsakanin kasar

Sin da kasar Rasha ya samu goyon bayan al’ummominsu matuka. Kana,

al’ummomin kasashen biyu suna ci gaba da karfafa mu’amala da fahimtar juna

a tsakaninsu, sakamakon wasu shirye-shiryen yin mu’amala da aka yi tsakanin

kasashen biyu, kamar shekarar al’adun Sin na kasar Rasha, da kuma shekarar

al’adun Rasha na kasar Sin, shekarar mu’amalar matasa a tsakanin kasar Sin

da kasar Rasha, da kuma shekarar mu’amala da hadin gwiwar wurare daban

daban a tsakanin kasashen biyu da dai sauransu.

A shekarar 2017, Sinawa masu yawon shakatawa kimanin miliyan 1.7 sun

ziyarci kasar Rasha, yayin da ’yan Rasha fiye da miliyan 2.3 suka zo yawon

bude ido a kasar Sin. Ban da haka, ya zuwa karshen shekarar 2016, yawan

daliban kasar Sin da suke karatu a Rasha hadi da yawan daliban Rasha da ke

neman samun karin ilimi a kasar Sin, ya kai fiye da dubu 70, adadin da ake

sa ran ganin karuwarsa zuwa dubu 100 a shekarar 2020. Yanzu a kasar Sin, a

duk wani kantin sayar da littattafai, za a iya samun littattafan da wasu

shahararrun marubutan kasar Rasha, irinsu Pushkin da Tolstoy, suka rubuta

cikin sauki. Sa’an nan a kasar Rasha, yayin da shugabannin Sin da Rasha

suka gana a garin Vladivostok, an nuna wani wasan kwaikwayon da masu

fasahar al’adu na kasar Sin suka tsara, a cikin gidan nuna wasannin

kwaikwayo na Mariinsky da ke birnin St Petersburg na kasar Rasha.

Hakika huldar dake tsakanin kasashen Sin da Rasha abin koyi ne ga sauran

kasashe, musamman ma ta fuskar kulla hulda tsakanin manyan kasashe dake

makwabtaka da juna. Wannan hulda mai kyau, ta kuma shaida nasarar da kasar

Sin ta samu, a kokarinta na yin hulda da sauran kasashe. Ta la’akari da

sakamakon da aka samu a wannan fanni, za a fahimci cewa, kalaman da Wang

Yi, mamban majalisar zartaswar kasar Sin kana ministan harkokin wajen

kasar, ya fada, tana bisa turba, inda Wang ya fadi cewa, bisa niyyar da

shugabannin kasashen Sin da Rasha suka nuna ta kyautata huldar dake

tsakanin kasashen 2, jama’ar kasashen na ta kokarin kulla kauna da samun

fahimtar juna tsakaninsu, abin da ya rika karfafa huldar dake tsakanin

kasashen 2. (Masu Fassarawa: Lubabatu Lei, Bilkisu Xin, Bello Wang, Maryam

Yang, ma’aikatan sashen Hausa na CRI)

Advertisement

labarai