An bayyana kyakkyawar Alakar shugaban ma’aikatan fadar Gwamnatin Jihar Kano, Dakta Ali Haruna Makodo, da cewa itace tasa muka Karrama shi. Sharif Ahmad Shu’aibu shugaban Majalisar Muryar Malaman Gandujiyya sannan kuma masawarci na musamman kan Harkokin makarantun Allo ne bayyana haka ga Leadership Ayau Jim kadan da mika lambar girmamawa a Kano.
Da yake gabatar da jawabinsa alokacin bikin mikar shaidar Karramawa, Sharif Ahmad Shu’aibu ya bayyana cewa dalilin Karrama shugaban ma’aikatan fadar Gwamnatin Jihar Kano Dakta Ali Haruna Makoda shi ne kyakkyawar dangantakarsa da malamai, wanda wannan kyakkyawar fahimta ce tasa ake samun fahimtar juna tsakanin malaman da Gwamnati.
Da yake tsokaci kan nasarorin da ofishinsa na mashawarciyar na musammann kan harkokin makarantun Allo ya cimma, ya bayyana cewa Ofis din nasa ya samar da takunkumin Fuska mai tarin yawa domin taimakawa kokarin Gwamanti na dakile yaduwar annobar a Kano. Haka kuma mun samu nasarar sayawa matasa fama faman shiga makarantar harkokin tsaro, samawa malamai gurabun aikin yi da kuma samar da wakilcin wannan ofis a yankunan masarautun Jihar Kano biyar.
Da yake gabatar da jawabinsa bayan karbar lambar girmamawar, Dakta Ali Haruna Makoda ya bayyana farin cikinsa da samun karramawa daga Malamai magada annabawa, wannan zai kara zaburar damu wajen hada kai da wannan kungiya fomin tabbatar da ganin ana yin aiki tare.