Kyakkyawar Dangantaka Tsakanin Kansilolin Karamar Hukumar Nasarawa Na Bunkasa Yankin – Hon. Saleh Kwamanda

An bayyana nasarori da ake samu na dinbin ayyukan cigaba da raya kasa da gina al’umma da ake gudanarwa a Karamar hukumar Nasarawa nada alaka da irin kyakkyawar dangantaka da ake da ita tsakanin majalisar zartarwa da karamar hukumar karkashin jagorancin Hon. Lamin Sani da majalisar Kansiloli da Hon. Sale Kwamanda yake jan ragama a matsayin Kakakinta.

Ita dai Karamar hukumar Nasarawa tayi fice a wajen gudanar da ayyuka a fannoni daban-daban na raya kasa a karkashin shugaban karamar hukumar Hon.Lamin Sani da yake jagorancinta a karo na Biyu na tabbatar da yanda kyakkyawar alaka a tsakanin masu ruwa da tsaki a gudanar da mulkin yankin ke tafiya.

Da yake zantawa da wakilimmu Shugaban majalisar Kansilolin na Karamar hukumar Nasarawa Kansila mai wakiltar Mazabar Tudun Murtala, Hon. Saleh Kwamanda ya tabbatar da cewa akwai kyakkyawar alaka da majalisar kansiloli da yake jagoranta da majalisar zartarwar karamar hukumar wanda kuma shi ne silar cigaban al’umma da ake samu.

Ya kara da cewa yana ganin duk wannan cigaba da ake samu yana tare da da alaka da irin addu’oi na fatan alhairi da kuma hadin-kai da al’umma ke musu domin kuwa a matsayinsu na majalisar Kansiloli tunda suka zo basu taba samun rashin fahimtar juna ba tare ma akai ga cewa za’a cire wani, kullum burinsu yaya za’a bijiro da abinda zai kawo cigaban al’umma,wannan shine a gabansu.

Ya ce, irin fadi-tashi aiki tykuru da jajircewa da shugaban Karamar hukumar Lamin Sani wanda kuma shi ne shugaban ALGON na jihar Kano, yake a kodayaushe yana dada bunkasa cigaban yankin.

Hon. Saleh Kwamanda ya yi nuni da cewa Jagororinsu na siyasa a karamar hukumar basu taba yin katsalandan a al’amarin shugabanci tsakanin majalisar Kansiloli da Majalisar zartarwar karamar hukumar ba.

Ya ce, wani abin farin ciki shi ne Allah ya azurta kusan duk yan siyasa na karamar hukumar Nasarawa mutanene masu kima da tarbiyya da mutuntaka da baza kajisu a cikin wani al’amari da bai kamata ba.

Hon. Saleh Kwamanda ya ce, bayan yaci zabe a mazabarsa na Tudun Murtala aka zabe shi a matsayin kakakin majalisar Kansilolin Nasarawa ran 15/2/2018 ya yi ya rataya Kur’ani da yin alkawari kullum inya tuna wannan yana samun kwarin gwiwa yin aiki tukuru dan sauke nauyin al’umna.

Ya ce, a matsayinsa na dan siyasa daya fito daga gidan siyasar Mataimakin Gwamnan Kano Dokta Nasir Yusuf Gawuna da suke fatan Allah ya tabbatar da fatan da suke masa na daga Liman sai Na’ibi a jihar Kano a 2023 yana koyi dashi wajen aiki tukuru dan sauke nauyin al’ummar Karamar hukumar Nasarawa.

Yace a yankin mabarsa ta Tudun Murtala yana gudanarda ayyuka da suka hada da na raya kasa da bunkasa cigaban al’umma ta bada tallafi na abinci da yin aikin ido da ayyukan magudanan ruwa da tallafawa cigaban ilimi da dinbin muhimman ayyuka

Hon. Saleh ya ce duk abinda ake Allah ne ke basa ikon ayi ba watk dabara ba domin yana duban bawa da zuciya ne dan haka duk wani abu na alkhairi daya aiwatar akayi yabo akai yakanji dadi ya kuma godewa Allah daya bashi ikonyi.

Sannan sai ya yi kira ga al’umma da cewa babu cigaba da zai samu bada hadin-kan al’umma ba.Shugabanci kuma Allah ke bayarwa in akace wane shine shugaba Allah ne ya bashi dan haka a hada-kai dan a sami nasara.

Kakakin majalisar Kansilolin na karamar hukumar Nasarawa ya yi kira ga al’ummar Jihar Kano akan su cigaba da baiwa Gwamnan Jihar Kano, Dokta Abdullahi Umar Ganduje da mataimakinsa Dokta Nasiru Yusuf Gawuna hadi-kai da goyon baya ta addu’a da fatan alkhairi domin cigaba da basu nasarar kyautata cigaban jihar Kano da al’ummarta.Ya kuma yaba da irin goyon baya da abokan aikinsa kansiloli ke bashi koda wani lokaci.

 

 

Exit mobile version