Connect with us

RAHOTANNI

Kyakyawar Alakar Fadar Shugaban Kasa Da Majalisa Ta Kawo Ci Gaba A Shekara Daya – AYC

Published

on

Shugaban Kungiyar gamaiyyar Matasan Arewacin Nijeriya AYC Kwamarade Muhmmad Mukhtar  ya yi nuni da cewa, ci gaban da aka samu a Nijeriya a cikin shekara daya ya samu ne saboda kyakywan fahimtar dake a tsakanin  Fadar Shugaban kasa da Majalisar Dattawa a karkashn Shugabancin Shugaban Majalisar Sanata Ahmed Lawan.

Kwamarade Muhmmad Mukhtar a hirarsa da Leadership Ayau a Kadun, ya sanar da hakan ne kan cika shekara daya  akan karagar Majalisar Dattawa da  Shugaban Majalisar Sanata Ahmed Lawan ya cika a jiya Alhamis ya ce, “Kamar yadda nake fada a kullum, bama yabon abinda ba haka yake ba, a saboda haka, muna da yakinin cewar, kyakyawar fahimta a tsakanin Fadar Shugaban kasa da Majalisar Dattawa ce ta sanya aka samu manyan ci gaba a kasar nan baki daya ta bangarori da ban da ban”.

A cewar Mukhtar, a jawabin da Sanata Ahmed Lawan ya yi bayan an zabe shi Shugaban Majalisar  Dattawa ya ce, dole ayi aiki kafada da kafada tsakanin Majalisar Dattawa da da Fadar Shugaban kasa in har ana son a ci gaba, kuma yau a kasar nan, babu wanda zaice ba’a samu ci gaban ba, musamman a cikin shekara daya da Sanata Lawan ya yi akan Karagar ta  Shugaban Majalisar Dattawa ba.”

Mukhtar ya yi nuni da cewa, ba dan bullar annobar Korona a Nijeriya ba, da sai yan Nijeriya sunga ci gaba mai dimbin yawa a karkaahin Shugabancin Sanata Ahmed Lawan, inda ya kara da cewa, duk abinda aka kawo a gaban zauren Majalisar Dattawa daga bangaren Shugaban kasa,  Sanata Lawan yana tabbatar da yan Majalisar sunyi dubi kan hakan a cikin lokaci don aiwatarwa.

“Muna godewa Allah yau shekara daya ke nan da Sanata Ahmed Lawan ya zama Shugaban Majalisar Dattawa ba bu wani rikici a Majalisar domin  ya jajirce wajen  yiwa kasa da yan kasa aiki tukuru don a samar masu da ci gaban da zai amfane ya kuma amfani kasa baki daya”.

Shugaban na AYC sanar da cewa, a yanzu ne Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya san cewa, Majalisar Dattawa ta yi shugaba jajirtacce, mai kishin kasa da kuma alummarta baki daya.

Da yake yin tsokaci kan jihar Yobe da Sanata Ahmed Lawan ta fito Kwamarade Muhmmad Mukhtar ya ce, mutanen jihar suna alfahari da Sanata Ahmed Lawan domin ya kawo masu ci gaba ta fannoni da dama da suka intanta rayuwar su.

A cewar Kwamarade Muhmmad Mukhtar, a kwanan baya Shugaban Majalisar ta Dattawa ya sanya an duba lafiyar masu fama da larorin rashin lafiya kyauta harda duba lafiyar dabbobi.

Kwamarade Muhmmad Mukhtar ya kara da cewa, bayan bullar annobar Korona a kasar nan,”  Banga inda aka taimaawa alumma ba a jihohin kasar nan, kamar a yankin Sanata Ahmed Lawan ba, domin da aljihunsa ya yi wannan taimakawa alummar yankin nasa”.

Kwamarade Muhmmad Mukhtar ya ce, ba’a taba yin Shugaban Majalisar Dattawa a Nijeriya mai son jama’a  kamar Sanata Ahmed Lawan ba.

A karshe, Kwamarade Muhmmad Mukhtar ya yi kira ga daukacin yan Nijeriya, musamman matasa suci gaba da wanzar da zaman lafiya da kuma kawo abinda zai ciyar da Nijeriya da yan kasar gaba.

 

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: