Yusuf Shuaibu" />

Kyari Zai Gurfana Gaban Majalisa Domin Ba’asin Cinikin Danyen Man Tiriliyan N3.878

Kyari

A yau Alhamin ce, shugaban kamfanin mai ta kasa (NNPC) Mista Mele Kyari ake sa ran zai bayyana a gaban majalisar wakilai domin bayar da ba’asi a kan naira tiriliyan 3.878, harajin kudaden dayan mai da ka sayar a cikin gida Nijeriya. Sauran bayanan kudaden da zai bayar da bayani a kan sun hada da bayanin kudaden gas na wasu watannin tun a shekarar 20, wanda shugaban kamfanin NNPC zai amsa tambayoyin ‘yan majalisa da suka hada da yadda yadda aka dawo wa kamfanin NNPC naira biliyan 450 daga cikin asusun tarayya da kudaden da aka dawo da su na naira tiriliyan 1.8 da kuma harajin da ba a biya ba na gas na dala 198,919,212.27 kwatankwacin naira 37,189,084,819.19 ba tare da yin bayani ba.

Haka kuma, ana tsammanin Mista Kyari zai gabatar da bayani akan korafe-korafe kan biyan kamfanin gas ta kasa a cikin asusunsa na dala 30,963,894.01 kwatankwacin naira 16,099,887,119.77 tare da na kasuwancin hadaka na dala 292,094,405.82 akwatankwacin naira 2,474,295,000. Duk wannan bai kare ba, majalisar ta bukaci zai gabatar da bayanan asusun kamfanin da bayanin ma’aikatan da suka yi rityaya da bayanan asusun bankin kamfanin da kudaden da ya biya kamfanin gas ta kasa. Haka kuma, ana sa ran shugaban NNPC zai yi bayanin wadanda suke amfana da asusun kamfanin gas ta kasa da kamfanin ayyukan makamashi da kungiyoyin ayyukan man fetur da kamfanin da ke rarrab mai a Nijeriya. a bangare daya kuma, zai yi bayanin wuraren da kudaden kasuwancin hadaka suke zurarewa da bankin asusun kasa da kasa da kuma bayanan biyan kudaden bashi da aka biya a cikin asusun kasa da kasa.

Shugaban kamfanin zai yi bayanin korafe-korafen kudaden da suka bace a kasuwancin hadaka na dala 292,094,405.82 kwatankwacin naira 2,474,295,000. Za a bukaci shugaban kasa da ya nuna wa majalisa dakardar amincewar shugaban kasa a kan rarraba kudade mallakar kamfanin NNPC da sauran dukkan kudade makamantan wadannan.

A cikin takardar kiran gayyatar da majalisar ta yi wa shugaban kamfanin NNPC mai taken, kwamitin majalisar wakilai mai kula da asusun gwamnati wanda dan majalisa, Oluwole Oke yake jagoranta, ya rubuta shafi biyu na takardar wasika mai lamba HR/PAC/SCO5/9NASS/FA/2015/1 a ranar 1 ga watan Fabrairun shekarar 2021, wanda yake bukatar shugaban kamfanin NNPC ya bayyana a gaban kwamitin mai kula da asusun gwamnati domin amsa wadansu taimayoyi. Sauran abubuwan da za a bincika sun hada da bayanan kan asusun kasuwancin hadaka da ayyukan da kamfanin NNPC ta gabatar tun daga shekararb 2014 har zuwa shekarar 2015, inda za a bukaci ya bayar da bayanan kudaden da kamfanin ya kashe a wannan shekaru da kuma harajin gas wanda ba a biya ba na dala 198,919,212.27 kwatankwacin naira 39,189,084,819.19.

A cewar kwamitin, a kalla kamfanoni 26 suke amfana da kudaden tare da shugaban kamfanin.

“Kwamitin yana bukatar gudanar da aikinsa da tsarinb mulki ya daura masa wajen kulawa da kudaden gwamnati da bayar da bayanan kudaden da aka kashi kamar yadda sashi na 80 da 85 da 88 da 89 na kundin tsarin mulkin Nijeriya wanda aka yi wa garanbawul ya tanada. Inda majalisar wakilai mai kulawa da asudun gwamnati take da ikon gudanar da bincike bisa rahoton da ta samu na asusun tarayya na shekarar 2015.

“A lokacin zaman shekara tare da akawun gwamnatin tarayya a ranar Juma’a 29 ga watan Junairun shekarar 2021, kwamitin ya samu nasarar warwar wasu matsaloli da dama da suka tasho, wanda shi ne mukaddashin da ya rubuta wa shugaban kamfanin NNPC wasikan gayyata mai shafi biyu. Hakazalika, kwamitin ya bayar da nunu da doka mai lamba HR/PAC/SCO5/9NASS/FS/2016, wanda ya gabatar da jawabi a ranar 2 ga watan Fabrairun shekarar 2021 ga shugaban kamfanin NNPC, domin gabatar masa da rashin gabatar da takardun shaidar bayanan kudaden kamfanin mai ta kasa a shekarar 2016. Kwamitin ta samu dukkan wadannan korafi ne a cikin rahoton bayanan kudade shekarar 2014 da aka gabatar wa majalisa na kamfanin.

Exit mobile version