Connect with us

Uncategorized

Kyau Da Tasirinsa

Published

on

Abu mai kyau, a takaice yana nufin dukkan abin da yake da dadin kallo. Ko wanda ake nishadantuwa idan aka kalla ko rabar shi. Haka kuma idan maganar sheka ake yi, abu mai kyau zai iya zama mai dadin kamshi, ko mai dadin sauti, idan maganar ji ake yi.
Kyau, a tsakanin mutane duk da ra’ayi kan sha bamban, akwai mutumin ko matar da daga ka yi mata kallo daya za ka yarda lallai kyakkyawa ce! Wannan abu ne da ya ba bukatar wani janjani.
Kyau abu ne mai muhimmanci, kuma dukkanmu muna son kyau. Abin da muka fi so shi ne, a ce mu ne muke da kyan, sannan abokan zamanmu na aure sannan ‘ya’yanmu. Mutum ba zai zama abin zargi ba don yana son mai kyau. Saboda abubuwa da dama da mutane masu daraja an kawata su da kyau.
Abin farin cikin da yake tattare da lamarin kyau, shi ne: Kowa ma zai iya zama kyakkyawa! Watakila kuma abin bakin cikin da ke tattare da shi shi ne: Kowane mai kyau ma zai iya zama mummuna!
Malamai suna raba kyau zuwa iri biyu, cewa akwai:
1. Al jamalul zahir da
2. Al jamalul badin.
Aljamalul zahir ko physical beauty, shi ne kyan da za ka gan shi kuru-kura da idanunka. Misali, da kallon Dawisu a lokacin da ya baza jelarsa za ka tabbatar wa kanka cewa kana kallon wani abu mai kyau. Haka kuma abin yake idan ka kalli mai kyau daga cikin mutane.
Wannan kyau ba abin gudu ba ne, shi ya sa ma duk muke rububinsa. Alfanonsa kuma yana da matukar yawa. Domin yakan shafi kusan dukkannin harkoki da mu’amulolinmu na yau da kullum.
Dale Archer ya ce: “Bincike ya tabbatar da cewa, idan kamfanunuwa biyu masu yin kaya iri daya suna kasuwanci. To wadanda suka sa kyawawan mata a gun sayar da kayan sun fi cin riba. Saboda an fi sayan nasu.”
Ya kuma kara da cewa: “Kyawawan mutane sun fi samun kulawa daga jama’a. An fi saurin ba su gudunmawa yayin da suka nemi taimako. An fi yi musu murmushi. Sun fi samun samari kyawawa ko attajirai.”
Haka ne kam. To amma ya kamata kuma mu fahimci wasu muhimman abubuwa da suke tattare da sha’anin kyakkyawar suffa. Wadanda watakila sanin sun zai iya amfanar da mu.

Jamalul Badin
Shi ne kyan da yake a boye. Wanda ba za ka gan shi a kan fuska ko surar mutum idan ka kalle shi da idanunka , kamar jamalul zahir ba. Wata tambaya da mutane suka rika yi a game da wannan kyan ita ce: “Shin me ya sa ma za a yarda da cewa wannan kyau ne, alhalin kuma an ce ba a ganinsu a fili kamar na farko?”
Mafi saukin amsar da za ka bayar ita ce: Dama babban abin da kyau yake janyowa shi ne farin jini, wato a so mutum kuma ya sami wata kima ta musamman darajar wannan kyan. Don haka za ka iya kiran mutumin da wani dalili ya janyo mar farin jini da sauran abubuwan da kaykkyawan mutum yakan samu a albarkacin kyansa cewa shi ma mai kyau ne.
Haka kuma za ka iya cewa, ai dama babu wani abu muhimmi a jikin mutum da ya fi nagarta. Don haka nagarta ita ce kyau kawai. Ba ka lura da macijiya ba ne, tana da kyau amma kowa yana tsoron rabar ta!
Wasu dalilai da za su sa mu yarda da wadannan hujjoji su ne: Sau da dama mukan manta da batun kyau, mu shagaltu da son wani ko wata mai karancin kyan sura, saboda yana da ko tana da nagarta ko kyawawan halaye ko ilimi da makamantansu.
Malamai sun ce nagarta da kyakkyawan hali ne suke sa wa Allah SWT Ya so
mutum, daga nan sai kowa ya manta da muninsa ya shiga son sa. Bisa la’akari da hadisin nan da yake cewa: “Idan Ubangiji SWT Yana son mutum, sai Ya umarci Mala’iku da su yi shela wa halittun sammai da na kasa cewa Allah Yana son wane, don haka ku ma ku so shi!” To daga wannan lokaci ne sai wani boyayyen kyau ya lullube mutumin, har sai ka ga kowa shi yake rububi, tare da cewa a can baya ana sane da cewa ba wani mai kyan sura ba ne!
Wannan kuwa shi ne dalilin da ya sa suke cewa, kowane mutum ma zai iya zama kyakkyawa idan ya so. Amma kafin wani karin bayani game da yadda za mu iya zama kyawawa, bari mu dubi hangen da wasu suke da shi game da illa ko rashin ta da kyan kan iya haddasa wa mai shi.

Shin Kyau Yana Da Wata Illa?
Hakika masana da yawa sun tafi a kan cewa kyan mutane da yawa yakan sa su su kasance marasa dadin zamantakewa a lokuta da dama. Sai dai ba za a ce dukkannin kyawawan ne kuma za su iya kasancewa haka ba, amma dai akwai kaso mai yawa.
Lokacin da Dr. Archer yake zayyana irin karramawa da nasarorin da kyawawan mutane suke samu, daga karshe sai ya ce: Hakan yana janyowa su dauki kansu fiye da ainishin yadda suke, sakamakon kambamawar da suka saba ji ana yi musa. Sai kuma su fara ganin sauran gama-garin mutane a matsarin masu karancin muhimmanci. Sannan su nemi komai nasu ya zama ana yi musu shi a mafi karramawar yanayi. Don haka kana iya cewe duk mai kyan da ya tabbata a haka ba shi da saukin mu’amula kenan.
Malam Jafar Mahmud ya ce: “Sau da yawa mata masu karancin kyau sun fi saukin sha’ani da juriyar hakuri a zaman aure. Saboda abin da suke tunanin an rage su da shi, da ya kamata su cike gurbinsa da nagarta. Yayin da kyawawan mata sukan kasance masu karancin saukin kai a lokuta da dama. Domin idan tai kwalliya ta zauna a gaban madubi ta kalli kanta ta yi murmushi, sai ta ce ai ko ka sake ta ma yanzu idan ta fita wasu ne za su ci gaba da rabubin ta.”
Sau da dama wannan tunanin shi ne yake hana wasu daga ckin mata masu kyau iya juriyar zama da miji. Saboda hangen damar da suke da ita ta samun wani cikin sauki.
Dr. Frederic Nueman yana ganin sau da yawa idan zama ya yi zama mutum yakan mance da batun kyan, ya koma ganin macen a matsayin ta na mace kawai. Ya ce kuma da yawa daga cikin kyawawan sun fara gane hakan na faruwa. Yana cewa: “Wata kyakkyawar mata ta taba gaya min cewa: Banbancin na wani dan karamin lokaci ne, amma daga an zauna abubuwan da suke a boye ne suke tasiri, ba kyan ba.”
Sannan rayuwar kyawawan mutane ta fi tsada a kan ta masu karancin kyau. Domin wasu suna ganin yawanci kyawawan mata suna karar da kaso mai tsoka na kudin da suke samu a kokarinsu na ci gaba da tattalin kyan nasu, don kar ya samu tasgaro.
Sannan sau da dama kyan yakan zama barazana ga masu shi. Dr. Archer ya ce “Sau da yawa wasu matan ba sa son kawance da su, saboda tsoron
kar su yi musu kwacen saurayi.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: