Connect with us

WASANNI

Kyautar Naira Dubu 100 Ga Duk Dan Wasan Da Ya Zura Kwallo A Ragar [Masu Gida]

Published

on

Dan wasan baya na tawagar kwallon kafa ta Nijeriya, Super Eagles, Shehu Abdullahi ya yi alkawarin bai wa kungiyar kwallon kafa ta Sokoto United kyautar kudi idan suka ci Kano Pillars.

A wani sakon bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Twitter, Abdullahi ya yi alkawarin bai wa kungiyar ta Sokoto naira 100,000 kan kowace kwallon da ya ci idan ya samu nasara a kan kungiyar Kano Pillars.

Sakkwato United za ta kara da Kano Pillars a wani wasa na gasar cin kofin kalubale na Aieto Cup wanda aka fara bugawa tun ranar biyar ga wannan watan.

Dan wasan, wanda a yanzu haka yana buga wasa a kungiyar Bursaspor ta Turkiyya, ya ce ya dauki wannan matakin ne domin nuna goyon bayansa ga tsohowar kungiyarsa wadda yabuga wasa yana matashi.

Duk da cewa Abdullahi ya taba buga wa Kano Pillars wasa, dan wasan ya ce ya yi sakon bidiyon ne ga hukumar gudanarwa da kuma ‘yan wasan kungiyar Sokoto United.

“Ga duk wani kwallon da kuka ci kano Pillars tare da nasara, zan ba ku naira 100,000 sannan Idan kuka ci kwallo biyu za ku samu 200,000, idan kuka ci uku za ku samu 300,000. Idan za ku iya cin biyar zuwa goma, zan ba ku kudinsu.” In ji Shehu Abdullahi

Dan wasan dai ya yi wasa a Sokoto United da Kano Pillars da Kasida FC na Kuwait kafin ya koma buga wasa a Turai a kasar Turkiyya

Sokoto United dai ta fitar da MFM, da ke buga gasar Firimiyar Najeriya, a gasar kafin wannan karawar da za ta yi da Kano Pillars yayinda Kano Pillars kuma ta doke kungiyar Ngwa United.

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: