Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
ADVERTISEMENT
Home RIGAR 'YANCI

Kyautata Wa Makiyi Na Da Daga Sunnar Ma’aiki – Hafiz Abdullah

by Sulaiman Ibrahim
March 16, 2021
in RIGAR 'YANCI
2 min read
Kyautata Wa Makiyi Na Da Daga Sunnar Ma’aiki – Hafiz Abdullah
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Daga Mustapha Ibrahim, Kano

 

An bayyana cewa, Sunnar Manzon Allah (SAW) na da yawa kuma tana da fadi, domin ba sai wacce take daidai da buktarka ba ta zama sunna da zaka yi, a’a, kyautata wa makiyi ma da nuna masa akasin kiyayya na daga cikin sunnar Manzon Allah (SAW).

Bayanin hakan ya fito ne daga bakin fittacan matashin malami addinan Musulunci kuma sha’iri, wato Shugaban Gidauniyar Ambato Wacce aka fi sani da ‘Ambato Foundation’ da babban ofishinta ke Kanon Dabo, Malam Hafiz Abdallah, a lokacin taron bude masallaci da wata baiwar Allah, Hajiya Aisha, wacce aka fi sani Sayyada Azimi, ta gina a unguwar Danbare dake Kano, wanda a ka gabatar a ranar Asabar da ta gabata.

“Za ka ji an ce mutum yana sa fararen kaya ko yana cin nama da makamantansu, sai a ce sunna ce. Wannan gaskiya ne, amma kyautata wa makiyinka na daga cikin sunnar Ma’aiki, domin shi ne mafi kyawun dabi’a da kyakkyawar mu’amala mafi kyau da Allah ya yi masa kuma aikinsa abin koyi ne bisa umarnin Mahallici kuma an aiko shi ne, don cika kyawawan dabi’u da mu’amala mafi kyau,” in ji sha’irin mai bege.

Har ila yau ya ce, “makasudin wannan taro na yau na bude masallaci da makaranta karkashin jagorance wannan gidauniya ta Ambato Foundation shine, isar da sako na Manzon Allah (SAW), kamar yadda Manzon ya ce, ya bar ma na abubuwa biyu; wato Alkurani Mai Girma, da kuma Ahlin Ma’aiki, wanda ya ce idan muka tsaya akan wannan koyarwa tasa ba za mu bace ba.

“To, don haka shi Musulunci kamar yadda ya zo a wani hadisi shine, Musulmi nagari shi ne wanda Muslimi suka kubata daga sharrin harshensa da hannunsa.”

Ita ma Hajiya Aisha, wacce aka fi sani da Sayyada Azimi, wacce ta gina wannan katafaren masallaci da aka yi wa lakabi da Masallacin Sayyada Aisha Mai Dakin Manzon Allah, ta kara da cewa, an gina shi ne, don kaunar Manzon Allah kuma komai ta mallaka na ma’ikin Allah ne.

 

SendShareTweetShare
Previous Post

Rokonmu Ga Al’umma Domin Cimma Nasarar Tsarin Kwali Jari

Next Post

Mun Manta Da Rashin Nasararmu Kan FC Porto, Cewar Ronaldo

RelatedPosts

Zamfara

Gwamnatin Jihar Zamfara Ta Tabbatar Da Kama  Wasu Sojoji Masu Hulda Da ‘Yan Ta’adda

by Muhammad
2 days ago
0

Daga Hussaini Yero, Gwamnatin jihar Zamfara ta tabbatar da rahotan...

Kansila Mai Mataimaka 18 Ya Sadaukar Da Albashinsa Na Farko

by Sulaiman Ibrahim
3 weeks ago
0

Daga Abdullahi Muh’d, Kano Shugaban Gidauniyar ‘Charity’ mai rajin tallafa...

APC

Sanata Al-Makura Ya Cancanci Rike Kujerar Shugabancin APC, Inji Gwamna Sule

by Muhammad
3 weeks ago
0

Daga Zubairu M Lawal, A yayin da uwar jam'iyyar APC...

Next Post
Duk Duniya Ba Wanda Ya Kai Cristiano Zura Kwallo A Kungiya Da Kasarsa

Mun Manta Da Rashin Nasararmu Kan FC Porto, Cewar Ronaldo

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version