Kyautata Wa Makiyi Na Da Daga Sunnar Ma’aiki – Hafiz Abdullah

Daga Mustapha Ibrahim, Kano

 

An bayyana cewa, Sunnar Manzon Allah (SAW) na da yawa kuma tana da fadi, domin ba sai wacce take daidai da buktarka ba ta zama sunna da zaka yi, a’a, kyautata wa makiyi ma da nuna masa akasin kiyayya na daga cikin sunnar Manzon Allah (SAW).

Bayanin hakan ya fito ne daga bakin fittacan matashin malami addinan Musulunci kuma sha’iri, wato Shugaban Gidauniyar Ambato Wacce aka fi sani da ‘Ambato Foundation’ da babban ofishinta ke Kanon Dabo, Malam Hafiz Abdallah, a lokacin taron bude masallaci da wata baiwar Allah, Hajiya Aisha, wacce aka fi sani Sayyada Azimi, ta gina a unguwar Danbare dake Kano, wanda a ka gabatar a ranar Asabar da ta gabata.

“Za ka ji an ce mutum yana sa fararen kaya ko yana cin nama da makamantansu, sai a ce sunna ce. Wannan gaskiya ne, amma kyautata wa makiyinka na daga cikin sunnar Ma’aiki, domin shi ne mafi kyawun dabi’a da kyakkyawar mu’amala mafi kyau da Allah ya yi masa kuma aikinsa abin koyi ne bisa umarnin Mahallici kuma an aiko shi ne, don cika kyawawan dabi’u da mu’amala mafi kyau,” in ji sha’irin mai bege.

Har ila yau ya ce, “makasudin wannan taro na yau na bude masallaci da makaranta karkashin jagorance wannan gidauniya ta Ambato Foundation shine, isar da sako na Manzon Allah (SAW), kamar yadda Manzon ya ce, ya bar ma na abubuwa biyu; wato Alkurani Mai Girma, da kuma Ahlin Ma’aiki, wanda ya ce idan muka tsaya akan wannan koyarwa tasa ba za mu bace ba.

“To, don haka shi Musulunci kamar yadda ya zo a wani hadisi shine, Musulmi nagari shi ne wanda Muslimi suka kubata daga sharrin harshensa da hannunsa.”

Ita ma Hajiya Aisha, wacce aka fi sani da Sayyada Azimi, wacce ta gina wannan katafaren masallaci da aka yi wa lakabi da Masallacin Sayyada Aisha Mai Dakin Manzon Allah, ta kara da cewa, an gina shi ne, don kaunar Manzon Allah kuma komai ta mallaka na ma’ikin Allah ne.

 

Exit mobile version