La liga Ta Yi Mana Nisa

Barceolna

Dan wasan tsakiyar kungiyar kwallon kafa ta Barcelona, Sergio Busquets ya yi amannar cewar damar kungiyarsa, tasa ta lashe gasar La Ligar bana ta gushe bayan da suka buga canjaras 3-3 da kungiyar Levante a ranar Talata.

Barcelona na jan ragamar wasan na Talata da kwallaye 2 -0 kafin a tafi hutun rabin lokaci daga Lionel Messi da Pedri, amma sai bakin suka yunkuro suka farke wadannan kwallaye bayan an dawo ta hannun Gonzalo Melero da Jose Luis Morales.

Duk da cewa Ousmane Dembele ya dora Barcelona a turbar nasara da kwallo ta 3 da ya ci, Sergio Leon ya farke a minti na 83 da wasan kuma a haka aka tashi daga wasan babu wadda ta samu nasara.

Wannan sakamako ya sa Barcelona a bayan masu jan ragamar gasar, kuma ya sa maki daya ne tak tazararsu da abokan hamayyarsu Real Madrid, kuma dukkanninsu na da kwanten wasa daya.

kungiyar kwallon kafa ta Atletico Madrid ta kara shiga gaban Barcelona a ranar Laraba bayan ta doke kungiyar kwallon kafa ta Real Sociedad a wasan da suka karbi bakuncinsu a birnin Madrid.

Real Madrid kuma za su samu damar shigewa gaban Barcelona idan suka yi nasara a ziyarar da za su kai gidan kungiyar kwallon kafa ta Granada a yau Alhamis a wani wasa mai hatsari da kungiyoyin zasu fafata.

Busquets ya ce makin da suka rage ‘yan kalilan ne, kuma, samun nasarar lashe gasar ga kungiyarsa zai ta’allaka ne ga abin da abokan hamayyarsu suka yi a wasanninsu na nan gaba da zasu fafata.

 

Exit mobile version