A jiya Alhamis Rukunin Kamfanonin LEADERSHIP ya gudanar da babban taronsa tare da ba da lambobin yabo ga Gwarazan mutanen da suka yi fice a fannoni daban-daban a shekarar 2018.
An yi bikin ne a Babban Dakin Taron Cibiyar Duniya da ke Abuja a jiya Alhamis. Ga wasu hotunan hidindimun taron:
Shugaban Rukunan Kamfanonin LEADERSHIP, Mista Sam Nda-Isaiah yana jawabin maraba a wurin taron.
Daga hagu:Shugaban Kamfanin TAK Continental Limited, Mista Thomas Etuh yana karbar lambar yabon Gwarzon Maáikacin Gwamnati na shekarar 2018 daga Alhaji Ahmed Joda.
Gwarzon Dan wasan nishadi na shekara, Obinna Simeon (wanda aka fi sani da MC Tagwaye), yana karbar lambar yabonsa daga hannun wakilin Ministan Abuja, Alhaji Bashir Mai-Bornu a wurin taron.
Daga hagu: Wakilin Gwamnan Jihar Kogi, Barista Ibrahim Sani (SAN), yana karbar lambar yabon da aka baiwa gwamnan jihar a matsayin Gwarzon Gwamna a shekarar 2018 daga daga Ministan Muhalli, Suleiman Hassan.
Daga hagu: Daraktan Kamfanin Kera Motoci na Innoson, Chinasom Chukwuma (a tsakiya) tana karbar lambar yabon da aka baiwa kamfanin bisa jaruntakar shugabansa wurin gudanarwa daga hannun shugaban taron kuma Jakadan Nijeriya a Amurka, Mai Shariá Sylbanus Nsof, a tare da su akwai shugaban sashen hulda da jamaá na kamfanin, Mista Cornell Osigwe.
Manajan Daraktan Bankin Bunkasa Aikin Gona, Malam Kabiru Mohammed Adamu yana karbar lambar yabon Gwarzon Maáikacin Banki na shekarar 2018 daga Ministan Muhalli, Suleiman Hassan.
Daga hagu: Manajan Daraktan Kamfanin Sufurin Jiragen Sama na Azman, Alhaji Umar Abubakar yana karbar lambar yabon da aka baiwa kamfanin a matsayin Gwarzon Kamfanin Sufurin Jiragen Sama na shekarar 2018 daga Kwamishinan Hukumar INEC, Mista Festus Okoye
Daga hagu: Tsohon ministan ruwa, Mista Obadiah Ando yana karbar lambar yabon Gwarzon Gwamna na shekarar 2018 a madadin Gwamnan Taraba, Darius Ishaku daga shugaban Rukunin Kamfanonin LEADERSHIP, Mista Sam Nda-Isaiah.