Labarin Bawa Dorugu: Bahaushen Farko Da Ya Fara Zagaya Turai

Cigaba daga makon jiya

Daga Sadik Tukur Gwarzo

Dorugu ya ci gaba da bada labari cewa, “Barebarin nan sai da suka ba ni suna. Daya ne a cikin su ya tambaye ni cewa, mene ne sunanka? Na ce masa Dorugu, suka ce sunanka ‘Barka-ganna’ da yaren Borno. Suka raba gidan da muke ciki biyu dakin maza da na mata, bayi suna daga cikin lolloki amma babu hanyar wucewa har sai sun zo ta bakin kofar ubangijinsu. Ni kuwa koda yaushe ina tafiya wajen su, ina yin zance da su muna yin dariya da wargi. Ni kadai ake baiwa wannan damar domin a lokacin ba ni da wayo sasai.

Kowace safiya idan na zo wucewa, sai ubangijina ya ce da ni “Barka-ganna mai dundufa.” Na kan yi dariya na wuce wurin mata bayi. Amma ubangijina na da wata

baiwa Sadaka, ita ce babba a cikin dukkanin mata bayi. Rannan da na tafi wajen su da yamma, sai ta kira ni, ina tsammanin za ta fada min maganar alheri ne, ashe

lalata take son yi da ni. Ta ce da ni, na zo, na ce na ki, ta ce, saboda me? Na ce, ban sani ba, ta ce, kana jin tsoro ne? Na ce, kawai ina so in fita ne. Kememe ta hana ni fita, ta ce idan ka fita sake ka fada wa wani, sai na yi maka duka. Na ce da ita, babu wandzan fadawa.

Bayan kwana daya ko biyu ne na ji za a aike ni Borno. Na ce, ni za a aika Borno? Suka ce kwarai da gaske, na ce, ya yi kyau. Suka ba ni tasa na zuba ruwa, suka dora ni a kan doki suka tafi tare da ni muna ta sauri saboda suna so su iske wadansu mutane da ke tare da shanu.

Idan doki ya yi gudu, sai ka ji ruwan da ke cikin gora yana kara bulum-bulum, sai su hau dariya, suna yin yaren Borno.Ni kuwa ban san me suke cewa ba, na zamo tamkar kurma. A haka har muka tarar da mutanen da ke tare da shanu, suka dora ni a kan wani Sa, a nan ne na samu wani saurayi yana yin magana da Hausa, muka yi ta fira da shi har muka isa Borno.

Da muka shiga Borno, sai na ga ashe babban gari ne. Suka shigar da ni wani gida, na ga matar Ubangijina fara ce tar, sunan birnin Borno Kukawa, daga zinder zuwa Kukawa tafiya kwana ashirin ce a kafa, tafiyar doki kuma kwana goma.Matar Ubangijina tana da diya ‘yar shekara hudu, dukkanin su kuma suna sona. Suna da bayi masu yawa. Amma diyar matar Ubangijina komai ta ci tana ba ni saura, a nan sai wani ciwo ya kama ta mai suna, Agana, ta zauna ba ta da lafiya sai ni ne ke zama kusa da

ita, komai take so ina kawo mata. Akwai kuma wata baiwa tsohuwa, ita ce ke kula da  bayi, ita ma tana zagayawa wajen diyar Ubangijina, mu uku muka rika zama a wajen ta har ta samu lafiya. Rannan ina daga cikin daki kusa da bakin kofar gida, na hau tona kasa, ina tsammanin zan samu ajiya, sai na tarar da wani abu mai karfi daga karkashin sauran tukunya. Na fitar da shi na bude, sai na ga ashe kudi ne, da na ga kudin na da yawa, ban ciri komai ba sai na ruga na tafi na kira tsohuwar nan na ce da ita, ga kudi na samu amma ban san ko na wane ne ba, ina magana da Hausa. Ita kuwa ba ta jin Hausa, sai na ja ta na nuna mata, ta dauki kudin duka, ina tsammanin ko sun kai Naira dari, amma dai Naira takwas ta ba ni a cikin kudin, ashe kudin na wani mutum ne, ta tafi kasuwa ta yo siyayya da su.

Ya aka yi-ya aka yi, masu kudi suka tambayi tsohuwar nan ina kudi, sai ta ce da su, ni ne na dauka, ni kuwa na ce musu na ga kudi amma na ba ta, ita kuma ta dauki Naira  takwas ta ban i daga ciki, nan suka zauna ba su ce komai ba. Wata rana, na tafi gidan wata mata ‘yar garinmu, tana da yaro mai jin hausa, amma bayan sun koma sun fara mantawa. Sai matar Ubangijina ta gan ni ina yin magana da shi, ta yi tsammanin ina so na gudu ne, daga nan ne ta dauki rigata ta daure a jikin zaninta, ni kuma na yi ta kuka jikina yana yin rawa saboda tsoro, ta cewa, danta da yaren Borno “Ke ger kude sukagere” ma’ana kawo mari ka daure shi, a lokacin ni ma na fara jin yaren na Borno. Da na ji danta ya shiga cikin daki yana taba mari, ina rawar jiki na kwance daurin da ta yi min a sannu, sannan na durkusa na rika ba hakuri ina neman tuba, ga shi ba ta jin yaren Hausa. Ala tilas aka nemo wata baiwa mai jin Hausa na yi mata bayanin duka abin da ya faru, sannan ita ma ta yiwa Uwargijiyata bayani, kana suka rabu da ni.

Haka na zauna babu aikin da nake yi, sai daga baya ne aka mayar da ni zuwa gari wajen wani sabon gida da ake ginawa, aka hada ni da bayin Ubangijina, a nan ne nake daukar kasa tare da su suna yin ginin gida. Wani lokacin mukan tafi kiwon dawaki da

maraice mu koma gida, wani lokacin kuwa cikin gari ake tura mu mu dauko tuwo mu zo mu ci. Da yaren Borno sukan kira sunan tuwon ‘’Brigashi’’. Ko tuwo babu miya muna hada shi da gishiri mu ci, don kowa na da gishiri a aljihunsa, tuwon da aka ci shi da gishiri kuwa, yafi mai miya dadi. A haka har Ubangijina ya karaso Borno daga

zinder tare da wasu bayi masu yawa. Yana tafe ana buga kalangu har cikin gari. Da ya sauka mu ka je muka gaishe shi, sannan muka dawo inda muke yin aiki.

Bayan kwana biyu sai wani yaronsa yake labarta min cewa, Ubangijina zai ba da ni saboda bashi, na ce da kyau, dama na ga wani Bature yana zagayowa. Ashe kuwa

Baturen za a baiwa ni.

( A wannan lokacin Dakta Bath da ‘yan tawagarsa suka isa Borno a tarihin tafiyarsu)

 

Za mu cigaba a mako na gaba in sha Allahu

Exit mobile version