Labarin Haduwata Da Maman Bariki

Assalamu alaikum ‘yan uwa da abokan arziki ma’abota karanta wannan jarida mai farin jini da tarin albarka LEADERSHIP A YAU LAHADI barkanmu da sake saduwa a cikin wannan fili namu na ADABI A YAU, filin da yake kawo muku rahotanni a kan duniyar rubutu da marubuta, game da halin da duniyar ke ciki, gwagwarmayar marubuta da ma gajerun labarai, wani lokacin ma rubutacciyar waka, har ma da hira da marubutan don cikakken tarihinsu.

A yau Lahadi filin zai kawo muku tsaraba ne ta gajeren labari daga fasihi matashin marubuci MUTTAKA A. HASSAN, wadda ya rubuta bayan dawowar sa daga Zaria a shafinsa na Facebook, a matsayin tsaraba ga makaranta da su ke biye da shi a shafin. Wanda dama marubuta su kan yi rubutu su ba da labarin wani abu da ya faru da su cikin sigar labari, wanda suke cakuda shi da hikima da basirar da Allah ya ba su don nishadantar da makaranta da kuma wa’azantarwa.

Muttaka ya yi wa tsarabar tasa take ne da Tafiya Mabudin Ilimi dogon labari ne da ya yi shi babi-babi. To a ciki ne za mu zo muku da babin da ya masa lakabi da Haduwata Da Maman Bariki. Da haka muke cewa a sha karatu lafiya.

 

Haduwata Da Maman Bariki

Ba komai ne ya kai ni Zaria ba sai gudanar da aikina na P.O.P CEILING, to da yake lokacin da mu ka sauka yamma ta yi hakan ya sa na fara fuskantar kalubale kamar; rashin sanin takamaiman wurin da za mu kwana kasancewar wanda ya san inda za mu yi aikin ya wuce kasuwa sayo kayan aiki, duhun daren da ya fara yi muna tsaye cirko-cirko tamkar Zakaru a sabuwar unguwar da babu zirga-zirgar al’umma, matsanancin sanyin da ya fara busowa, da kuma gabatowar sallahr Isha’i alhali ko Magriba ba mu yi ba. Muna tsaye na jiyo an kira sallah don haka na ce da su su jira ni na je na nemo ruwan al’awala.

A haka na fito na nufi wani lungu wanda iya hangena ban ga ko mutum daya ba balle na saka ran zan samu wurin sayar da ruwa, don haka na mike lungun sai da na je karshensa na sha kwana sannan na hango wata karamar tireda. Lokacin da na karasa wurin sai na tarar ana sayar da pure water don haka na sayi leda daya na taho da shi.

Ni da Kamal muka yi alwala sannan muka bar wa Tempul jiran kayanmu da yake Kirista ne muka wuce masallaci. Bayan sun sayo kayan aiki an kai mu wurin da za mu yi aiki mun shirya wajen kwanciya sai muka tafi neman abincin da za mu ci. Bakin flyober mu ka je, nan na bada cajin wayata sannan na fara kewaye ina neman abin da zan ci, a karshe dai da na ga duk abincin da ke wajen bai min ba dole na je wajen mai shayi na cika cikina.

Bayan kamar minti arba’in na je karbar cajina, ga mamakina sai na ji an ce wai kudin caji N50. A farko na za ta wasa yake; amma da na tabbatar da gaske yake sai na ba shi kudin muka tafi ina mamakin garin da na zo, domin hatta mai shayin da na sayi indomie daya da kwai biyu N250 na biya maimakon N200 da na saba saya a Kano.

Lokacin da muka yi kwana biyu a garin ne na ji garin ya fara fita daga raina saboda dalilai biyu: Na farko idan gari ya waye ba ma samun abinci sai mun yi tafiya mai nisan gaske kuma a kafa, na biyu idan rana ta yi babu wani abinci a kusa da mu sai dankali da yaji.Haka nan da daddare ma babu masu abinci sai mun je nesa, ni kuma bisa al’adata ba na son yawo a kasa idan na je aiki wani garin domin na san abu ne da zai karo min gajiya a kan wadda na kwasa ta aiki. Saboda haka na yanke shawarar daina fita neman abinci da safe, da na tashi da safe aiki zan fara sai rana ta yi zan karya.

Abin dariya a ranar da na kudurce wannan niyar a ranar na warwareta, domin tun sha daya da rabi na ga gidan ya fara juya min sakamakon matsananciyar yunwar da ke azabtar da ni, tilas na fito neman abin da zan saka a cikina don a zauna lafiya, to da yake ba na son zuwa nesa sai ya kasance ban nufi hanyar flyober ba na nufi wani wuri daban ashe rabon haduwata ne da matar da na sanyawa sunan Maman Bariki.

Tun a nesa da na hango wajen da take zaune na ga babu komai sai kasko da mai ana soye-soye jikina ya ba ni dankali ne don haka na sauya layi; amma ina sauya hanya ta fara kwalla min kira. Na so sharewa to amma da na tuna ba na jin dadi idan an share ni sai na juyo.

“Me P.O.P ba za ka zo ka sayi dankali ba za ka wuce?” Ta fada da murmushi a fuskarta. To da yake Hausawa kan ce wai shimfidar fuska ta wuce ta tabarma kawai sakin fuskarta sai ya sauya ra’ayina na je wurin na zauna, ta tambayeni na nawa za a ba ni na amsa da na N100. Haka aka ciko min plate da dankali da yaji da pure water biyu a gefe.

Cin dankalin kawai nake saboda ina jin yunwa, amma a zahirin gaskiya na tsani dankali, haka nan wani karin abin gundura ta saka ni a gaba sai surutai take yi min da wasu zantuka na batsa wadanda maimaita su ma rashin kunya ne, ko rabi ban ci ba na fasa ruwan na sha sannan na miki na dan yi nesa da wurin kadan sannan na dubeta shekeke na ce, “Dan matso ki ji wata magana.”

Na yi mamakin yadda ta taho tana wani karairaya ita a dole ga mace, mamaki ya kamani lokacin da na kare mata kallo, fara ce wadda kai tsaye mutum zai gane kankaro farin aka yi a dole, domin man da ta yi bilicin din da shi bai ba ta hadin kai ba kasancewar wani wurin ya yi dabbare-dabbare na baki musamman gabobin yatsun hannunta da wuyanta, kakkaura ce doguwa wadda ban kara gane tsayinta ba sai da ta zo ta tsaya a gabanana daga kai na sama na hangeta kwatankwacin kallon da akuya za ta yi kafin ta hango tozon rakumi, sanye ta ke da bakaken kaya kanana na riga da siket wadanda suka kama jikinta matuka, duk da ban san shekarunta ba amma ina da yakinin ta girmeni da shekaru masu yawan gaske domin a hasashena ta haura shekaru talatin.

Kodayake cikin kallo daya za ka gane ba Bahaushiya ba ce duk da dai alamu sun nuna musulma ce. “Nawa ne kudinki?” Na fada ina dubanta. “Naira dari.” “Kin ba ni ruwa biyu ai.” “Eh, ruwa kyauta ne.” “Ungo,” na mika mata dubu daya, “Kawo canji.” “Ayya ! Dan’uwa ba ni da canji sai dai ka je ka dawo.” Ta fada bayan ta saka kudin a wata karamar jaka da ke hannunta. “Ke da kudinki N100 shi ne zan bar miki dubu daya?” “Haba Dan’uwa kada ka damu ina nan har karfe shida na yamma, kuma ko ma ba wannan ba zan iya kwatanta maka gidana sai ka ciko mu zauna tare, ni kadai ce a gidana…”

Iya abin da na ji ke nan a furucin nata sai kiran marubuci Adamu Yusuf Indabo ya shigo wayata, bayan na amsa kira mun gama tattaunawa na dubeta cike da takaici tare da mamakin ragon azanci da shiririta irin tata, domin idan ban da shiririta ko da zan yi iskanci ai ba zan bi wadda ta girme ni da shekaru tsububu irin nata ba.

Mayar da wayata aljihu na yi sannan na fara magana ba tare da na dubeta ba, “Ba koya miki kasuwanci zan yi ba, amma a shawarce ki rika lura da irin yanayin kwastomanki sai ki san irin kalaman da za ki tare shi da su, idan ki na daukar duka maza daya ne har ki na taryarsu da kalamai na batsa irin wadannan wani idan ya zo ba zai kara zuwa ba kamar ni.”

Na tsahirta na dubeta na ga ta yi sakato tana kallona kamar tsoho ya ga aljani sannan na dora, “Abu na karshe shi ne, ki dauko kudina ki ba ni, idan kuma ba haka ba ni kuma a wannan lokacin zan nuna miki kalar nawa shaidancin.” “Me za ka yi min?” “Na san kin lura da cewa tun da na zo ban cewa kowa komai ba ko? To haka nake, ban cika magana ba sai dai akwai yanke hukunci maimakon doguwar magana,” na aro fuskar kunu na yafa sannan na dora, “Wallahi kin ji na rantse ko? Idan kika kara minti biyu kacal ba ki ba ni kudina ba sai na dauki matakin da zai saka ki mamaki tare da nadamar rike kudin da kika yi.”

Ban tsammaci za ta bada kudin ba ba tare da ta kara wani furuci ba, amma bisa mamakina sai ta zuge jakar ta dauko canji ta miko min. Na kirga kudi sai na iske N700, na bude ba ki da niyar yin magana sai ta rigani.

“Dan’uwa ka yi hakuri ka je ka dawo, wallahi iyakacin canjina ke nan.” Ban furta komai ba na juya na tafi ina mamakin abubuwa biyu: Na farko yadda mutane da dama ke kallon duk masu sana’ar P.O.P a matsayin ‘yan iska, na biyu yadda ta rada min sunan ‘dan’uwa ta yadda a kusan kowane furucinta sai ta kirani da sunan.

To na koma gidan da muke aiki sai na ki sanar da abokan aikina labarin haduwata da matar da na sanyawa suna maman bariki, saboda kamar yadda mutane ke zargin masu sana’armu da lalacewa tabbas na san akwai lalatattu a cikinmu ta yadda matsawar na ba su labari to fa sun samu wurin zuwa domin da ma wasu a cikinmu irinta suke nema. Karfe shida saura na wanke jikina na koma wajenta don karbar canjina.

A lokacin da na je sai na tarar da wajen akwai samari da dama wadanda cikin kallo daya na zargi ba mutanen kirki ba ne sakamakon ba su da wata siffa ko daya ta mutanen kirki, daga gefenta kuma wasu ‘yanmata ne su uku wadanda su ma da ka kalle su za ka gane jirgi daya ne ya kwaso su. Ban sani ba ko tun kafin na karaso ta ba su labarina, ni dai kawai na ga yadda ‘yanmatan ke min wani irin kallo mai wahalar ganewa.

“Dan’uwa ka dawo?” Ta fada tana murmushi, yayin da ni kuma na yi shiru ban tanka ba. Ta juya ta kalli wata baka gajeriya a cikin ‘yanmatan, “Ruki ba ni N200 a gurinki.” “To Aunty,” wadda ta kira da Ruki ta amsa sannan ta miko mata kudin ta karba ta ba ni na yi gaba a zuciyata ina raya babu abin da zai kara hada mu har na bar Zaria. Ashe abun da ban Sani ba shi ne, wannan haduwar tamu Ita ce mafari.

 

Exit mobile version