CRI Hausa" />

Labarin Wasu Tsoffi 2 Dake Iya Dafa Gahawa

A kauyen Wulong dake garin Langzhong na lardin Si’chuan dake yammacin kasar Sin, an kafa kananan otel-otel na saukar baki da yawa, sa’an nan wasu biyu daga cikinsu sun shahara a shafin Internet sosai, wadanda suke da sunayen “Su Qing” da “ Yun Zhen”.
Hakika an nada sunayen ga otel-otel din guda 2 ne bisa sunayen masu otel, wato Madam Wang Suqing, da Madam Du Yunzhen. Kafin haka, a shekarar 2017, mutanen kauyen mai suna Wulong sun tsaida niyyar raya kauyensu ta hanyar aikin yawon shakatawa, bisa la’akari da kasancewar kauyen a cikin yankin duwatsu, inda ake samun muhalli mai ni’ima. Daga bisani an yi hira da Madam Wang Suqing, da Madam Du Yunzhen, don samun amincewarsu kan shirin yiwa gidajensu kwaskwarima, gami da maida su otel. Bayan da suka yarda da shirin, an yi wata babbar kwaskwarima a gidajen nasu, inda aka kiyaye wani salon al’adu na gargajiya na gidajen, tare da kyautata muhallin zama dake ciki, ta yadda baki ’yan yawon shakatawa zasu ji dadin zama a cikin wadannan gidajen.
Madam Wang Suqing tana da shekaru 85 a duniya, kana Du Yunzhen a nata bangaren, tana da shekaru 76 da haihuwa. Yanzu suna taimakawa tsabtace muhalli, da wasu ayyuka na samar da hidimomi ga baki masu yawon shakatawa, tare da samun albashi na Yuan 500 a kowane wata. Ban da wannan kuma, sun koyi wata fasahar zamani, wato dafawa tare da samar da abin yin shayi na gahawa, ko kuma a ce kofi. Idan an shiga cikin otel, za a ga tsoffin 2 suna zaune a bayan teburi, suna shirya kofi, inda za su karbi baki da mika musu gahawar da suka dafa, abin da ya sa baki ke jin dadi da kwanciyar hankali, kamar yadda suke a gidajensu.
A cewar tsoffin, saboda sun tsufa, kunnensu bai iya jin magana sosai, kana da wuya su rike wani abu a zuci. Don haka su kan manta da matakan da ake bi wajen shirya abin hada shayin na gahawa. Amma sauran ma’aikatan dake aiki a cikin otel din suna da hakuri sosai, inda su kan koyar da su fasahar dafa kofi, lamarin da ya kwantar da hankalin toffin, gami da faranta musu rai. Sun ce da ma sun yi zamansu cikin kadaici, amma yanzu kowace rana ana samun baki a gidajensu, wadanda suke zuwa domin shan kofi tare da su, da hira da su, lamarin da ya sa suke jin dadi matuka.
Labarin Madam Wang Suqing da Madam Du Yunzhen ya shaida wani tsarin da ake bi a kauyensu a fannin kawar da talauci da raya tattalin arziki, inda aka yi kwaskwarima kan tsoffin gidaje na mazauna kauyen, sa’an nan an mayar da su wurin masaukin baki, don raya harkar yawon shakawata. Ta wannan hanya, kamfanonin yawon shakatawa suna samun kudi, sa’an nan za su raba wani kaso daga cikin kudin ga mutanen kauyen, lamarin da ya sa suke samun wani kudin shiga, da fitar da kansu daga kangin talauci, ba tare da fitowa daga gidajensu ba. (Bello Wang)

Exit mobile version